Wasu matan aure a jihar Imo sun gudanar da zanga-zanga a Owerri kan yadda ‘yan matan jami’o’i ke kwace musu mazaje.
Matan auren sun ce ‘yan matan na kwace musu mazaje ta hanyar saka kayan da ke nuna tsiraici.
An saka bidiyon zanga-zangar da wadannan mata suka yi a kafafen sada zumunta a yanar gizo.
Matan sun yi tattaki zuwa dakin kwanan dalibai mata inda suka ja wa ‘yan matan kunne da su guji saka kayan da bai kamata ba suna nuna tsiraicin su ko su fuskanci hukuncin da za su yi musu.
Matan auren sun ce daga yanzu za su rika cin taran Naira 10,000 akan kowace macen da suka kama ta saka kayan dake nuna tsiraicin su.
“Duk budurwar da muka kama ta saka kayan da bai dace ba za ta biya mu taran Naira 10,000 sannan idan ta ci gaba za ta biya Naira 20,000.
“Duk wacce ta ki biyan mu za ta fuskanci hukunci daga wurin mu.
PREMIUM TIMES ta samu bayanin cewa matan auren sun yi tattaki har zuwa dakin kwanan ɗalibai mata dake kwalejin kimiya da fasaha dake Nekede a Owerri.
Matan auren sun kuma nuna wa ‘yan matan irin shigar da za su riƙa yi.
Akwai manyan makarantun gaba da Sakandare biyar a Owerri inda a ciki akwai jami’o’i uku, biyu kwalejin kimiya da fasaha.