Dan takarar shugaban ƙasa a karkashin inuwar jami’ayya APC Rotimi Amaechi ya bayyana cewa samar da tsaro na daga cikin matsalolin da zai fara kawo karshen su idan ya zama shugaban ƙasa.
Amaechi ya ɗauki wannan alkawari ne a wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa ranar Litinin a Abuja.
Ziyarar Amaechi yankin Neja-Delta
“Rankashi dade ni dan Neja-Delta ne kuma ina da masaniya da matsalolin dake tattare da yankin domin na yi gwaman a daya daga cikin jihohin yankin.
“Na zo a matsayin wanda ke da masaniya kan matsalolin dake tattare da yankin da Wanda ya yi gwamna a yankin Neja-Delta sannan idan har kuka zabe ni na zama shugaban ƙasa Kuma tare da goyan bayan gwamnatin tarayya zan kwato wa Yenagowa filayen ta domin ganin mutanen Bayelsa sun mallakin filaye.
“Na zo ne domin na samu goyan bayan ku da mutanen ku domin ku mara mun baya a takaran shugabancin kasar nan.
“Ina mai tabbatar muku cewa zan kawo ci gaba idan har na zama shugaban ƙasa sannan ku za ku zama shafaffu ‘yan gaban goshin gwamnatin tarayya.
A nashi tsokacin shugaban kungiyar sarakunan gargajiya na jihar Bunaraye Agada na 10 ya ce suna murnan marabtan dan su kuma dan takaran da ke da niyar yin abin da ya kamata a kasar nan.
Shima shugaban jami’iyyar APC na jihar Dennis Otiotio ya ce suna farin cikin marabtan shugaban da ya tsaya tare da su musamma a lokacin da jihar ke fama da matsaloli.
“A dalilin haka Amaechi ba sai ya yi kanfe a Bayelsa ba domin da Bayelsa da Rivers daya ne sannan shi shugaba ne da aka tabbatar da iyawansa.
Discussion about this post