‘Yar takarar shugaban ƙasa a karkashin Jam’iyyar APC Uju Ken-Ohanenye ta bayyana cewa za ta gama da duka matsalolin Najeriya a cikin watanni shida idan har aka zabe ta.
Ohanenye ta fadi haka ne a taron karramata da kungiyar matan jihar Anambra ‘Nzuko Umuada Anambra Advancement Int’l Initiative (NUAAII)’ ta yi a Abuja ranar Laraba.
Ta ce maza da suka jagoranci kasar nan Kuma suke kan mulki har yanzu sun yi kokarin su wajen kawar da matsalolin da ake fama da su a kasar nan. Amma ta ce lokaci ya yi da za a bai wa mace dama a kasar nan
A ganin ta Najeriya na bukatar mace da za ta kawar da matsalolin da ake fama da su a kasar.
Ohanenye ta ce Najeriya na bukatar macen da za ta yi amfani da kwarewarta wajen kawar da matsalolin kasar nan kamar yadda take yi wajen tafiyar da gida.
” A dalilin haka ya sa na fito takarar shugaban ƙasa saboda na san isan da yi amfani da irin hikima da dabarun mu na mata kamar yadda muke yi a gidajen mu ina tabbatar muku komai zai zama tarihi a ƙasar nan tini zan gama da matsalolin kasar nan.
“Ina kuma kira ga sauran mata da su shiga siyasa a kasar nan sannan ina yaba wa wadanda ke cikin siyasa a yanzu haka.
Ta ce yawan matan da suka fito takara a zaben da za a yi a 2023 sun yi kadan domin har yanzu ana bukatan mata da dama su fito takara.
Ta yi kira ga deligate da shugabannin jami’iyoyi da su mara wa matan da suka fito takara baya musamman a zaben fidda gwani da za a yi kafin zaben 2023.
Mataimakiyar shugaban kungiyar NUAAII Mrs Rufina Suleiman ta ce sun karrama Ohanenye saboda kokarin da ta yi wajen inganta rayuwar musamman mata a ƙasar nan.