Maitaimakawa Gwamna Muhammad Badaru akan harkokin makarantun kasa da sakandire, Zakari Kafin-Hausa, ya sayi fom din takarar Danmajalisar Jiha Mai wakiltar Karamar Hukumar Kafin-Hausa.
Zakari Kafin-Hausa yana daya daga cikin matasa na gaban goshin gwamna Muhammad Badaru.
Ya bayyana bukatar yin takararsa a shafinsa na Facebook a yau Talata inda daruruwan ma’abota shafin suka yi masa fatan alkhairi da samun nasara.
Zakari zai fafata a zaben fidda gwani da Dan Majalisa mai ci Muhammad Na’eem, wanda ake sa ran zai fito neman kujerar a karo na biyu a zaben 2023.
Sauran sun hada da Tanimu Ismail; Ajje Ruba; da kuma Abdulwahab kuliya.