Tsohon shugaban hukumar EFCC, kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Nuhu Ribadu ya tsindima cikin kogin takarar gwamnan jihar Adamawa.
Ba wannan ne karon farko da tsohon shugaban EFCC din ya fito rakarar gwamna ba, ya fito takara a 2019.
Da yawa daga cikin mutanen jigar Adamwa da suka zanta da PREMIUM TIMES HAUSA sun jinjina masa bisa wannan shawara da ya ɗauka na fitowa takarra gwamna a jihar.
Alhassan Modi, wani mazaunin garin Yola ya shaida wa wakilin mu cewa ” Mutum irin Ribadu ba kasafai ake samun irin su ba a al’umma. Baya ga gogewar sa a aikin sa, yana da gaskiya da rikon amana.
” Jihar Adamawa ta yi babban sa’a da Allah yayi mutum irin Nuhu Ribadu a cikin ta. Ku duba yadda tsarin sa yake, ga dattaku da kamala,sannan ga sanin ya kamata.
” Nuhu Ribadu mutum ne mai tausayi da kyma kishin talakawa. Ba za a zalunci talaka a karkashin sa ba sannan kuma yana da kishin mutanen sa. Idan Allah ya bashi mulkin jihar Adamawa ba kawai jihar ba, Najeriya ma zata shaida domin da irin su za arika kwarance a duniya
Lauratu Munnir, wata fitacciya ƴar siyasa kuma mai kishin jihar Adamawa ta ce ” Duk da dai ni ba ƴar jam’iyyar APC ba ce amma kuma dalili ya sa dole in koma jam’iyyar saboda Nuhu Ribadu. Idan yau aka ce kana tare da mutum irin Ribadu abin alfahari ne gareka saboda tsari irin nashi.
Idan ba a manta ba Nuhu Ribadu ne ya ci kyautar mutumin da ya fi kowa gaskiya a Duniya ta shekarar 2019, kyautar da aka bashi a kasar Qatar saboda maida wa gwamnatin tarayya zunzurutun kudin sata da aka bashi toshiyar baki har dala miliyan 15.
Kasashen duniya na yaba masa sannan na bugun kirji da shi a matsayin mutum na farko mai irin wannan kishi da nahiyar Afirka ta taɓa yi.