Dan majalisan da ke wakiltar Kazaure/Roni/Yankwashi/Gwiwa a majalisar Tarayya, Gudaji Kazaure ya bayyana cewa da gangar aka murɗe masa zaɓe saboda gwamnan jihar Abubakar Badaru baya ƙaunar sa.
Gudaji ya shaida wa manema labarai a wata takarda da ya fitar ranar Litinin cewa abinda aka yi a Kazaure wasan kwaikwayo ne kawai irin na Hausa amma ba zaɓe ba.
” Da karfin tsaiya aka shirya yadda za a kada ni. Gwamna Badaru ya umarci duka ciyamomin ƙananan hukumomin da da na ke wakilta da su tabbatar an kada ni a zaben Fidda gwani.
” Duka delegates dina ba aamince musu su yi zaɓe ba, wasu ne dabam wanda gwamna Badaru da kansa ya zabo sune suka yi wannan zaɓe.
” Ban yi niyyar shiga zaɓen ba amma wasu aminai na suka tilasta ni in shiga zaɓen. Daga baya dai ba asamu abinda ake so ba.
Kazaure ya ce tuni ya aika da wasikar korafin sa ga uwar jam’iyyar APC da kuma hukumar zaɓe ta kasa domin a bi masa hakkin sa.
” Ku saurare ni ku gani, ba za a yi min walle-walle ba ina ji ina gani. Kawai wasan kwaikwayo ne aka yi a Kazaure ba zaɓe ba. Amma kuma za ku ga yadda karshen zata kasance, akwai sauran ɓalla a gaba.
Idan ba a manta ba Kazaure ya tashi da ƙuri’u 26 ne kacal a zaɓen fidda gwani da aka yi ranar Asabar a Kazaure.
Discussion about this post