Fitaccen makamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargaɗi wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na sauran ‘yan takara cewa su ne ke da alhakin sake jefa ƙasar nan ciki bala’in da zai ci gaba da dabaibaye ta, muddin su ka riƙa karɓar kuɗaɗe su na zaɓen ‘yan takarar da ba su cancanta ta.
Gumi ya yi wannan kiran a daidai ranar da PDP ke gudanar da gangamin zaɓen fidda-gwani na masu takardar neman shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar.
Ya ce matsawar za su sa zalama da kwaɗayin ‘yan kuɗaɗen da ba su taka kara su ka karya ba, har su ka zaɓi wanda bai cancanta ba saboda kuɗi, to ko ya hau mulki ba zai iya kawar da matsalolin da su ke addabar ƙasar nan ba.
Ana ci gaba da ƙorafin yadda dimokraɗiyya ke ƙara lalacewa a Najeriya, ganin yadda ake ta raba wa deliget maƙudan kuɗaɗe a wurin zaɓen ‘yan takara a faɗin ƙasar nan
Lamarin ya yi munin da har EFCC ta kai ga fara baza jami’an ta wurin taron gangami, domin lura da waɗanda za su yi walkajami da kuɗaɗe a wurin fidda gwani.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa akwai dalilan da su ka sa ta baza jami’an ta a filin wasa na ƙasa, inda ake zaɓen fidda-gwanin PDP a cikin daren nan.
Kakakin EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa PREMIUM TIMES baza jami’an na su, kuma ya ce “mun je wurin ne don mu ga yadda gangamin taron zai kasance na yadda za a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa.”
Da aka tambaye shi ko jami’ai nawa aka tura a Dandalin Gangamin, Uwujaren ya ce “a yanzu ba ni da adadin yawan su tare da ni.”
Dama dai Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Maina ya yi alƙawarin bin diddigin yadda jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ke kashe kuɗaɗen su wajen kamfen, sayen fam da kuma zaɓen fidda gwani.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES Hausa ta lura da cewa EFCC ta kasa yin komai wajen yadda aka riƙa sayen wakilan zaɓen ‘yan takara a matakai daban-daban na zaɓukan faɗin ƙasar nan a cikin ‘yan kwanakin nan.
Wakilin mu kuma ya lura da cewa duk wani hoɓɓasa da EFCC za ta yi a yanzu, ba zai samu yabo daga idon ‘yan Najeriya ba, ganin yadda hukumar ta kasa taka wa jigon APC Bola Tinubu burki a zaɓen 2019, lokacin da ya ciki motoci biyu maƙil da kuɗi daga banki, a jajibirin zaɓen 2019, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.
Sannan kuma a shekarar an yi ƙorafin cewa Gwamnatin Tarayya ta toshe ƙofofin yadda Atiku zai yi amfani da kuɗaɗe a lokacin kamfen, amma kuma EFCC ta ƙyale Tinubu ya jidi kuɗaɗe daga banki ya kai gida, domin biyan buƙatar cin zaɓe.
A zaɓen fidda-gwani na yau dai manyan ‘yan takara sun haɗa da Atiku Abubakar, Gwamna Nyesom Wike, Aminu Tambuwal na Sokoto, Bukola Saraki.
Discussion about this post