Wani mamba na jam’iyyar APC daga Kano, mai suna Sagir Mai Iyali, ya nemi kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC ya soke takarar Bola Tinubu, saboda a cewar sa, bai cancanta ba.
Mai Iyali ya aika wa Shugaban APC Abdullahi Adamu wasiƙar a ranar 17 Ga Mayu.
A cikin kwafen takardar ƙorafin, ya ce Tinubu tsohon Gwamnan Legas ya yi wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ƙarya a cikin 1999, lokacin da ya fito takarar Gwamnan Jihar Legas, inda ya ce ya yi digiri a Jami’ar Chicago ta Amurka.
Mai Iyali ya ce tilas kafin a bar Tinubu ya tsaya takarar shugaban ƙasa, sai ya tabbatar tare da kawo hujjar cewa tabbar ya yi digiri a Jami’ar Chicago ɗin.
“Mu na da hujjar cewa a cikin 1999 Tinubu ya yi wa INEC ƙarya a rubuce cewa ya yi digiri a Jami’ar Chicago ta Amurka. Kuma a cikin fam ɗin INEC da ya cika, haka ya rubuta a katardar rantsuwar faɗin gaskiya wato affidavit, ya ce ya yi karatu a can daga 1972 zuwa 1976.
“To a yanzu dai duk an tabbatar da cewa ƙarya Tinubu ke yi, domin ya kasa kare kan sa, bayan ya shaida wa INEC haka a ranar 20 Ga Disamba, 1999. Kuma ya rubuta wa kotu wannan iƙirarin na ƙarya, a Babbar Kotun Legas da ke Ikeja a ranar 29 Ga Disamba, 1998.”
A ƙarshe dai Mai Iyali ya nemi Kwamitin Tantance ‘Yan Takara ya soke Tinubu, domin ko an tantance shi an zaɓe ma, aikin banza aka yi, kotu za su garzaya a soke shi.
An dai tantance Tinubu tun a ranar Litinin wajen 7:30 na dare.
Yanzu dai ana jiran sakamakon tantancewa kenan, bayan an kammala tantance sauran a yau Talata.
Discussion about this post