‘Yan acaba sun kai wa rukunin gidajen ‘Same Global’ dake Dakwo, Lokogoma a Abuja hari.
‘Yan acaban sun kai wannan hari ne ranar Lahadi bayan wani mai mota ya bankaɗe wasu ‘yan acaba biyu inda har daya ya mutu sannan ya gudu ya boye a daya daga cikin gidajen wannan rukunin gidaje.
Cikin fushi ‘yan acaban sai suka kona babban kofan shiga rukunin gidajen tare da wasu kadarori.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja Josephine Adeh ta bayyana wa PREMIUM TIMES ta waya cewa babu gidan da aka babbake Kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke yadawa.
Adeh ta ce zaman lafiya ya dawo yankin da rukunin gidajen.
“A ranar 29 ga Mayu da misalin karfe 1:3 na rana wasu ‘yan acaba sun kai wa rukunin gidajen ‘Same Global’ dake Dakwo a Galadimawa hari amma rundunar ta dawo da zaman lafiya a yankin.
“Rundunar na kira ga mutane da su kwantar da hankulansu su kuma su ci gaba da harkokinsu sannan su riƙa gaggauta kawo rahoton wani abu na tashin hankali idan ya auku.
Idan ba a manta ba makonin biyu da suka gabata PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda rikici ya barke a kasuwar katako dake Dei-Dei a Abuja tsakanin ‘yan kasuwa da ‘yan acaba.
Akalla mutum biyar ne suka mutu a dalilin wannan rikici na kasuwar Dei-Dei.
Discussion about this post