Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ya yi bitar tunin yadda tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya taimaka aka kafa jam’iyyar APC, wadda albarkacin ta ne shi Badaru ya zama gwamna a Jigawa cikin 2015.
Da ya ke jawabi a gaban wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na jihar Jigawa a ranar Juma’a a gaban Tinubu, Badaru ya ce da taimakon da Tinubu ya yi wa jam’iyyar ne ta kai shi ga samun nasara a Jihar Jigawa, cikin 2015.
“Mun nemi jam’iyyar da za mu shiga takarar gwamna cikin 2011. Asiwaju Bola Tinubu ya samar min jam’iyya. Na shiga zaɓe, na zo na biyu.”
Badaru ya ce duk da ya haɗu da ƙalubale a 2011, amma dai goyon bayan da ya samu a lokacin ne ya ƙara masa ƙaimin samun nasara a zaɓen 2015.
Badaru ya ce ya na cikin mutane ƙalilan waɗanda za su iya shiga har cikin ɗakin kwanan Tinubu, su tashe shi daga barci.
Ya ce akwai alaƙa mai ƙarfi da shaƙuwa ta ƙut-da-ƙut a tsakanin sa da Tinubu.
Ya ce su a Jigawa ‘yan ga-ni-kashe-nin Shugaba Buhari ne. Kuma za su iya yin duk abin da Buhari ya ce su yi. “Amma fa in dai son Buhari ne a ƙasar nan, to ba wanda ya kai Tinubu son Buhari.”
Ya ce duk wasu surutai da ake yi kan titi, na shirme ne, domin babu wanda ya san iyakar alaƙar da ke tsakanin Buhari da TInubu.
Jawabin Tinubu A Jigawa: Zan Kayar Da Badarun Ku A Wurin Zaɓen Fidda Gwani, Ku Zaɓe Ni Kawai:
Da ya ke jawabi, Tinubu ya ce duk da ya san Badaru ya fito takara, to zai kayar da shi a zaɓen fidda gwani. Don haka su zaɓe shi kawai.
Wannan furuci na sa ya birge ɗimbin jama’ar da ke wurin ana ta kuwwa da tafi. Wasu na “Sai Asiwajun Legas”. Sai Jagaban Bargu.”
“Gwamna Badaru ɗan uwa na ne. Tare mu ka fara ACN. Hakan ba ya na nufin ba za mu iya yin takara ba. Ni da shi kamar tagwayen da aka haifa manne da juna ne. Ba mai iya raba mu sai ƙwararren likita.”
Kalaman Badaru Kan Tinubu Sun Yi Karo Da Furucin Sa Kan Amaechi:
2023: Ba Zan Iya Takara Da Amaechi Ba, Saboda Ni Da Shi ‘Uban Mu’ Ɗaya -Gwamna Badaru:
Gwamna Muhammad Badaru na Jigawa ya bayyana cewa ba zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa shi da Rotimi Amaechi a ƙarƙashin APC ba.
Da ya ke jawabi gaban wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa a Dutse, a gaban Amaechi, Badaru ya ce a shirye ya ke ya janye wa Ministan Sufurin Najeriya takara, shi Badaru ɗin ya haƙura.
“Wasun ku na san sun fara tunanin cewa Badaru ma ɗan takarar shugaban ƙasa ne. To amma ina tabbatar maku cewa ba za a yi takara tsakani na da Amaechi ba, saboda ni da shi uban mu ɗaya (Shugaba Muhammadu Buhari). Kuma duk mu na girmama uban na mu. Na tabbata kuma za mu tafi ne a kan turba da alƙibla ɗaya.
“Ni da shi duk yaran Shugaba Muhammadu Buhari ne, kuma ya na son mu ƙwarai da gaske. Don haka duk abin da za mu yi, sai da neman tubarrakin sa.
“Don haka ku wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC na Jigawa, idan ku ka tuna da ni, to kuma ku tuna da Amaechi, saboda ni da shi duk ‘ya’yan Buhari ne.
“Saboda haka a ranar zaɓen fidda-gwani, ko dai na fito takara, ko kuma shi ya fito. Amma dai tabbas ba zan iya yin takara da shi ba, gara na janye masa.”
Tun da farko tsohon Minista Amaechi ya roƙi wakilan zaɓen ‘yan takarar APC na Jigawa su zaɓe shi, saboda ya cancanta. Ya ce ya fi sauran ‘yan takara sanin Najeriya.
Ya ce idan za a kalle shi, to a dube shi da abin da ya yi a baya, ba abin da ake yaɗawa a matsayin ji-ta-ji-ta a kan sa ba.
Discussion about this post