Kakakin ɗan takarar shugaban kasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya yi karin haske game da abinda ya wakana a ɗakin tantance ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ake yi yanzu haka a Otel ɗin Transcorp.
Onanuga ya ce kwamitin ta bukaci Tinubu yayi mata bayani kan dalilan da ya sa ya ke so ya shugabanci Najeriya da irin abubuwan da ya shirya wa kasar idan ya zama shugaban kasa.
” Anan ne Tinubu ya feɗe biri daga kai har wutsiya, inda ya bayyana yadda iya takun sa da sanin harkokin bunƙasa tattalin arzikin kasa ya sa ya Legas ta zama gagarimar jiha a ƙasar nan.
” Tinubu ya ciccibi jihar Legas daga kasa ya lula ta can kokoluwar sama ta hanyar tara kuɗaden shiga, abinda ba a taba yin irin sa ba tun kafuwar jihar.
” Baya ga kwarewa da ya ke dashi a harkar bunƙasa tattalin arzikin kasa, Tinubu ya goge a sanin yadda ake gudanar da ayyuka don cigaban al’umma.
A takaice dai amsoshin da Tinubu ya baiwa kwamitin ya burge su matuka.
Tinubu na daga cikin ƴan takara sama da 20 da jam’iyyar APC za ta tantance wanda kuma za su fafata a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar.
Waɗanda aka tantance sun hada da Emeka Nwajuiba; Gwamna David Umahi na Ebonyi, Felix Nicholas, Ibikunle Amosun; Gwamna Abubakar Badaru, Ajayi Borroffice, Ken Nnamani, Uju Ken-Ohaneye, Rotimi Amaechi; Sani Yerima da Tunde Bakare, a cleric.