Shugaban Majalisar Harkokin Musulunci a Jihar Akwa Ibom, Hassan Sadauki, ya zargi Gwamna Udom Emmanuel da laifin nuna bambanci ga Musulmai da Hausawa mazauna jihar tsawon shekaru masu yawan gaske.
A ranar Laraba ce Sadauki ya shaida wa wakilin mu cewa Gwamna Emmanual har yau ya ƙi kafa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Akwa Ibom tun da ya zama gwamna cikin 2015.
Dalilin haka ne inji Sadauki ta sa dukkan Musulmai daga Jihar Akwa Ibom, idan za su tafi Hajji, sai dai su tafi Kuros Riba ko Ribas su tashi daga can.
Jihohin Kuros Riba da Ribas dai duk su na da Hukumar Jin Daɗin Alhazai, amma banda Akwa Ibom.
Sannan kuma Sadauki ya ce tun da Udom Emmanuel ya zama Gwamna, ya daina gayyatar Musulmai zuwa yi masa gaisuwar Sallah, wadda kafin ya zama gwamna ana yin haka kafin 2015.
“Hatta ziyarar da mu kan kai wa gwamna ma a lokacin wannan gwamnan ya hana mu zuwa. Musamman bayan kammala azumi idan an yi Sallah. Gwamna ya soke tun da ya hau mulki cikin 2015, har yau ba a sake yi ba.” Inji Sadauki.
Sadauki ya ce shi da wasu Musulmai sun tuntuɓi Mataimakin Gwamna na Musamman kan Al’amurran Addini, Daniel Akwatang, amma har yau babu abin da ya canja.
Shi ma Kakakin Majalisar ta Al’amurran Addinin Musulunci a Akwai Ibom, Ahmed Isa ya tabbatar da wannan saniyar-ware da Gwamna Emmanual ya mayar da Musulmai da kuma Hausawa a Jihar su.
Isa ya ce gwamnatin Emmanual ta maida su saniyar-ware, babu kulawa, babu kayan inganta rayuwa a yankin unguwar su.
Amma hadimin gwamna mai suna Akwatang da su ka ce sun tuntuɓa, ya shaida wa wakilin mu cewa ya isar da wasiƙar su a hannun Gwamna, don haka ya sauke na sa nauyin.
Amma daga nan ya ƙi amsa duk wata tambaya da wakilin mu ya yi masa.
Sadauki ya shaida wa wakilin mu cewa tun tashin sa ya na ƙaramin yaro ya ke zaune a Akwai Ibom.
Ya ce a can ya yi firamare har jami’a, kuma ‘yar jihar Akwai Ibom ya ke aure, har sun haihu uku.
Wakilin mu ya je unguwar da Musulmai da Hausawa ke zaune a gefen birnin Uyo, babban birnin Akwa Ibom. Kuma ya ga babu wani abu da za a iya cewa gwamnatin jihar ta tsinana a unguwar.
Sai dai kuma mazauna unguwar har da shi Sadauki sun gode ganin yadda su ke zaune lafiya, ba a kai masu hari ko farmaki.
Su na zaune a kusa da inda aka yi mayanka ta zamani da kuma kasuwar sayar da shanu da raguna, tun cikin 2006.
A unguwar babu ruwan sha, babu titi kuma babu kyakkyawan tsarin wuraren zubar da shara.
Amma dai Shugaban Hukumar Tsafta da Kwashe Shara, Prince Ikim, ya shaida wa wakilin mu cewa nan da kwanaki biyar za a kwashe sharar da ke damun mutanen unguwar da wari.
Sadauki ya zargi Gwamna Emmanual da iƙirarin cewa ya ce gaba ɗaya jihar Akwa Ibom duk Kiristoci ne. Ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Discussion about this post