‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum hudu a gidan faston cocin Katolika na St Patrick a Gidan Maikambo a karamar hukumar Kafur jihar Katsina ranar Laraba.
Maharan sun afka gidan cikin dare inda suka yi garkuwa da fastocin cocin biyu Rev. Frs. Stephen Ojapa, MSP da Oliver Okpara sannan da wasu yara maza biyu dake zama tare da su.
Zuwa lokacin da aka rubuta labarin masu garkuwa da mutanen ba su kira sun nemi a biya su kudin fansa ba.
Jami’in yada labarai na cocin Katolika dake jihar Sokoto Christopher Omotosho ya sanar da haka ranar Laraba da safe.
Omotoso ya yi kira ga mutane da su saka fastocin da yaran cikin addu’o’in su domin Allah ya dawo da su lafiya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka sace faston cocin Katolika na St Pius Alphonsus Uboh dake kauyen Ikot Abasi Akpan a karamar hukumar Mkpat Enin jihar Akwa-Ibom.
Maharan sun nemi a biya su kudin fansan Naira miliyan 100 kafin su saki faston.
Cocin ta biya kudi inda faston ya dawo gida bayan ya yi kwanaki hudu a hannun masu garkuwa da mutane.
Cocin ba ta fadi yawan kudaden da ta biya ba.
Daga nan ma masu garkuwa da mutane su arce da faston cocin ‘Solid Rock Kingdom’ John Okoriko a Ibekwe Akpanya.
Maharan suma sun nemi a biya su naira miliyan 100 kafin su saki faston.