” Muna tsaye a tsakiyar garin Damrisai kawai muka hangi mutane sun dos mu da gudun tsiya. Kafin mu ankara kuwa sai muka rika jin rugugin harsahi ta ko-ina. Daga nan sai muma muka arce. Allah dai yayi nuna da sauran rayuwa ne a gaba, amma da tuni mun zama gawa.” Waɗannan sume Kalaman da wani tsohon kansila da yayi hira da wakilin PREMIUM TIMES.
Ƴan bindiga sun afka wa kauyukan Sabon Garin Damri, Damri da Kalahe da karfe biyun rana daidai an sakko daga sallar Juma’a mutane kuma suna cigaba da shagulgulan sallah kamar yadda suka saba.
Wani mazaunin Damri Mu’azu Damri ya shaida wa waklilin mu cewa sun kan mai uwa dawabi ne duk wanda kwanandhi ya ƙare shikenan.
” Mafi yawa daga cikin waɗanda maharan suka kashe baki ne da daga kauyukan dake kurkusa da waɗannan garuruwa.
“Sai dai kuma zan yaba wa jami’an tsaro bisa kokarn da su yi a lokacin da suka iso garin Damri. Badun Allah ya sa sun shigo ba da waɗanda za a kashe sai sun fi yawan waɗanda aka sanar.
” Da jami’an tsaro suka buɗe wa ƴan bindigan wuta suka kora ne aka samu saukin abin. Da wuta tayi wuta fa hatta abinci da dabbobin da suka sace na jama’a duk suka watsar dasu suka arce.