Mazaunan kauyen Ruwan Bore dake karamar hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara sun tabbatar cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 11 a kauyen ranar Asabar.
Mutanen sun ce a dalilin harin mutane da dama sun ji rauni a jikkunan su.
Ruwan Bore kauye ne dake kusa da hedikwatar karamar hukumar Talata Mafara.
Wani mazaunin Talatan Mafara Mustapha Lawan ya ce maharan sun shigo kauyen a kan babura da misalin karfe 6:14 na yamma.
Ya ce maharan sun kewaye kauyen domin hana mutane fita sai dai kuma duk da haka da wasu sun sun arce daga kauyen.
“An kashe hawarwakin mutum 11 da ƴan bindigan suka kashe sannan mutane da dama sun ji rauni sanadiyyar wannan hari.
“Kauyen ta zama babu kowa saboda duk mutanen cikin kauyen sun gudu a dalilin ƴan bindigan.
Wata ma’aikaciyar babbar asibitin Talata Mafara mai suna Maryam ta ce an kawo mutum biyar daga kauyen Ruwan Bore da suka ji mumunar rauni asibitin.
Maharan sun biyo sawun shannun wasu Fulani ne
Wata majiya mai tushe a ofishin ‘yan sandan dake Talata Mafara ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindiga sun biyo sawun shanun wasu Fulani ne zuwa kauyen Ruwan Bore domin su sace su.
Yan bindigan sun afka kauye Bore nr saboda su kwashe shanun waɗannan makiyaya.
Discussion about this post