Hukumar Hana Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi, NDLEA ta bayar da ƙarin haske dangane da yadda ƙasurgumin mai safarar muggan ƙwayoyi Afam Utaku, abokin harƙallar Abba Kyari ya riƙa shigo da ƙwayoyi cikin Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Talata, ya ce Ukatu wanda ke da kusancin ƙut-da-ƙut da Abba Kyari, ya shigo da Taramol na Naira biliyan 22 a cikin wata ɗaya kacal.
Makonni biyu da su ka gabata, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda NDLEA ta cafke ƙasurgumin falken ‘Taramol’ ɗin naira biliyan 3 da Abba Kyari ke da hannu cikin karkatar da ita.
Hukumar Hana Safara da Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA), ta kama wani biloniya kuma ƙasurgumin ɗan safarar muggan ƙwayoyin da ya shigo da ‘Taramol’ na naira biliyan 3 da Abba Kyari ke da hannu a ciki.
NDLEA ta ce sunan biloniya kuma wanda ya shigo da ‘Taramol’ ɗin Afam Mallinson Emmanual Utaku.
Emmanual Utaku dai shi ne Shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies.
Wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a na hukumar, Femi Babafemi ya sanar a ranar Litinin cewa sun damƙe Emmanual Utaku a ranar 13 Ga Afrilu, bayan an sha faman ƙoƙarin kama shi ya na zillewa.
A ƙarshe dai NDLEA ta ce an kama shi a cikin wani jirgi a ƙaramin filin jirgin saman Murtala Mohammed na Legas, daidai lokacin da jirgin ke niyyar tashi da shi zuwa Abuja.
Babafemi ya ce masu bincike biloniya Emmanual Utaku shi ne ƙasurgumin mai shigo da ‘Taramol’ samfurin 120mg, wato ƙarama, matsakaiciya ta 200mg da babba ta 225mg da kuma mafi girma ta 250mg, dukkan su kuma su na bugarwa.
Babafemi ya ce Emmanual Utaku ya mallaki wata masana’antar sarrafa magunguna da robobi, wadda ya ke amfani da ita matsayin bagaraswa ya na harƙallar shigo da muggan ƙwayoyi cikin Najeriya.
“Sannan kuma ya na da asusun ajiyar kuɗaɗe a banki har guda 103, waɗanda ya ke amfani da su ya na karkatar da maƙudan kuɗaɗe ƙasashen waje.
“Jami’an NDLEA sun fara sa-ido kan Emmanual Utaku cikin shekarar da ta gabata, bayan da aka ƙwace kayan biyar ba ‘Taramol’ daga hannun wani ma’aikatacin sa, a ranar 4 Ga Mayu, 2021.
An damƙe ma’aikacin ne lokacin da ya je zai sayar wa wasu ‘yan sandan da suka yi shigar-burtu ‘Taramol’ ɗin.
‘Yan sandan dai yaran Rundunar Kyari ce ta IRT da ke Ikeja, Legas.
“An yi ciniki tsakanin su za su sayi kowane katan ɗaya naira miliyan 17, maimakon naira miliyan 18 zuwa 20 da ake sayar da shi a kasuwar tsaye, a Legas.
“Bayan an kama ma’aikacin Emmanual Utaku su biyu, Pius Enidom da Sunday Ibekwete, sai waɗanda aka kama ɗin aka tasa ƙeyar su suka kai yaran Abba Kyari zuwa rumbun ajiyar ‘Taramol’ ɗin Emmanual Utaku da ke unguwar Ojota a Legas, inda aka kwaso katan 197 na ‘Taramol’.
“An ƙiyasta kuɗin su zai kai naira biliyan 3.” Inji Babafemi.
Zargin Yaran Kyari Da Sungume Katan 190 Na Taramol:
Bayan makonni uku da kwaso katan 197 waɗanda aka haɗa da kayan 5 suka tashi katan 202, an ƙiyasta kuɗin su naira biliyan 3.
“Daga nan sai yaran Abba Kyari ‘yan sandan IRT suka miƙa mutum biyu da suka kama da kuma katan 12 na ‘Taramol’ ga Hukumar NDLEA ta Jihar Legas. Amma ba su ce ga sauran katan 190 ba. Su ka yi shiru abin su.
“Daga nan ba a ƙara jin yadda yaran Abba Kyari suka yi da katan 190 na ‘Taramol’ ba, har sai yanzu bayan wata 8 da hukumar NDLEA ta kama gogarma kuma biloniya Emmanual Utaku, a ranar 13 Ga Afrilu, 2022.
“Yanzu haka Abba Kyari da wasu abokan harƙallar sa kuma manyan zaratan sa huɗu lokacin ya na aikin ɗan sanda, su na fuskantar tuhuma kan aikata laifuka daban-daban a Babbar Kotun Tarayya, Abuja.” Inji Babafemi.
Sabon Bincike: Yadda Ukatu Ya Shigo Da Taramol Ɗin Naira Biliyan 22 Cikin Wata Ɗaya:
Ranar Talatar washegarin Ƙaramar Sallah, NDLEA ta fitar da sanarwar cewa Ukatu ya daɗe ya na safarar muggan ƙwayoyi na biliyoyin nairori a cikin ƙasar nan.
Hukumar ta ce ya na da masana’antar sarrafa magunguna, ko kuma wani kamfani da ya ke amfani da shi domin bagaraswa.
“A cikin watan Oktoba, 2019, Ukatu ya shigo da kwantina biyu ɗauke da katan 1,284 na Taramol, wanda kuɗin su ya kai Naira biliyan 22.”
NDLEA ta fitar da sanarwar a ranar 3 Ga Mayu, domin rufe bakin masu surutan cewa hukumar ba ta da wata hujjar kama Cif Ukatu.
NDLEA ta ce ta gano yadda ya shigo da Taramol ɗin ta naira biliyan 22, a lokacin da jami’an hukumar ke binciken alaƙar sa da Abba Kyari kan yadda aka shigo da Taramol ɗin Naira biliyan 3 a baya-bayan nan.
Hukumar ta ce za ta maka shi kotu nan ba da daɗewa ba, da zaran ta kammala bincike.