Gwamban jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa lokaci yayi da jihar Filato zata saka wa tsohon ministan sufuri, kuma dan takarar shugaban kasa Rotimi Amaechi bisa abubuwan alkhairin da ya rika yi wa jihar a kowani lokaci idan haka ya taso.
” Bayan haka ina so in sanar maka cewa duka tsoffin kakain majalisun jihohi da mambobin su duk sun amince kai Za su yi a zaben fidda gwani.
” A duk lokacin da batu kan da jihar Filato ya tasu a taron majalisar zartarwa kana kan gaba wajen ganin jihar Filato ta samu abinda take so ku akwai mu a wurin ko babu. Dole ne yanzu mu maida hankali mu kuma saka maka da kuri’un mu a zaben fidda gwani dake tafe.
” A cikin mutanen da ka aika karatu kasar China, akwai yan asalin jihar Filato 7. Yanzu haka muna jiran su su dawo mu ci moriyar Kaaratun su.
Jihar Filato gidan ka ne. Ka kwantar da hankalinka ka kuri’un mu kaf din sa na ka ne.
Discussion about this post