Tsohon gwamnan jihar Kebbi kuma daya daga cikin sanatocin da ke wakiltar jihar Kebbi a majlaisar Dattawa Adamu Aliero ya ce ya janye daga takarar sanata ne saboda matsin da takuara da neman tozarta shi da gwamnatin jihar ke so su yi.
” Kowa ya san irin yadda nake kokarin tabbatar da ganin APC ta yi nasara a jihar Kebbi amma abinda ke faruwa yanzu babakere kawai ake yi wanda gwamnan jihar ne da kansa yake yin haka.
” Zaben da za ayi ko akayi ba zaɓe bane na wakilan gaskiya wanda aka zaɓa. Wakilan da za su yi zaɓe wakilai ne qanda wamnan jihar da kansa ya zabe su ɗaya bayan ɗaya kuma wai sune za su yi zaɓe.
” Ba da ni za ayi haka ba. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa dole in yi hakuri da takarar da nakeyi na janye kawai in ba su wuri su ci karen du ba babbaka.
A karshe Aliero ya ce zai koma gefe ne ya cigaba da haɗa kan ƴan siyasa a jihar kafun nan kuma sai su san me za su yi nan gaba.
Ba tun yanzu sanata Adamu Aliero ba su ga maciji tsakanin sa da gwamnan jihar Abubakar Bagudu.
Hakan ya sa dan takarar gwamna jihar wanda yake daga ɓangaren su Aloero ne ya sha kasa a zaben fidda gwani da aka yi a jihar.
Discussion about this post