Kwamishinan ƴan dandan Kano Sama’ila Dikko ya dhaida wa manema labarai a Kano cewa ba Nomb bane ya tashi a kasuwar Sabin Gari, tukunyar Iskar gas ce ta yi bindiga ta fashe.
Dikko ya ce gaba daya shugabannin tsaron jihar sun isa wannan wuri a sabongari domin sanin da ganin ainihin abin da ya auku.
” Ga mu duka anan, jami’an tsaron dake ke kula da jihar munanan. Abinda ya faru shine tukunyar gas ce da ke dakin wani mai yin Welda ta fashe.
Kwamishina Dikko ya ce ana cigaba da bincike a kai.
An ji karar fashewar wani abu a unguwar Sabon Gari dake jihar Kano wanda mutane suka tsorata suka fara gujeguje. Iyaye kuma suka dunguma makarantu suna kwashe ƴaƴan su daga makaranta.
Wasu sun yi ta raɗe-raɗin wai bom ne aka tada a kasuwar, wasu kuma suna cewa ƴan ƙunar bakin wake ne ya tada bom.
Zuwa yanzu dai ana hako ginin da ya rufta domin ciro mutanen da suka makale a cikin gini.