A watan Disambar 2014, lokacin Gwamna Kwankwaso yana fafutukar neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, tafiyar gaggawa ta kama shi zuwa jihar Lagos don kulle-kullen yadda zai samu tikitin takarar.
Ana tsakiyar fafutukar neman tikitin takarar shugaban kasa a Ikko, sai aka tunatar da Kwankwaso cewa wa’adin fitar da ‘yan takarar sanatoci yana kurewa, kuma ga shi ba’a yi zaben fidda gwani ba a Kano ta Arewa.
Haka Gwamna Kwankwaso ya umarci mataimakinsa Dr Abdullahi Umar Ganduje (wanda ya fitar ‘yan kwanaki kadan a matsayin dan takarar gwamna) da ya koma Kano da shi da tsohon mataimakin gwamna Abdullahi T. Gwarzo da Barau Jibrin don fitar da dan takarar sanatan Kano ta Arewa.
Umarnin Kwankwaso a wancan lokacin shi ne a mara wa T. Gwarzo baya ya samu tikitin. Amma kash! A lokacin Ganduje ya fi son Barau Jibrin ya samu kujerar. Haka kuwa aka yi, Ganduje ya jagoranci ‘delegates’ su ka sutale T. Gwarzo don Barau ya samu tikitin.
Tabbas Ganduje yana cikin tsaka mai wuya. A ra’ayi na bai kamata a ce gwamna ya yi shekara takwas a karagar mulki amma tikitin takara a jam’iyyar da ya je har kotun koli ya ya kwato ba ya gagare shi. Ni a gani na akwai nauyi a ce gwamna mai ci ya janye takararsa ya ba wa wanda shi ya yi silar kasancewarsa sanatan tun farkon fari ba. A hakikanin gaskiya Ganduje ke bin Barau bashi a siyasa, kuma Modibbon da na sani, ba zai yafe ba; sai ya karta masa manjagara ranar zabe.
Ni ina ganin zaman Barau ba zai haifa masa da mai ido ba, domin ta-ciki-na-ciki. Zai yi biyu babu ne, domin Ganduje da mukarrabansa ba su manta da adawar da ya yi ba lokacin yana tare da Shekarau.
Bugu da kari, Barau yana da abokan hamayya irin su Murtala Sule Garo a shiyyar Kano ta Arewa, kuma na san zai wuya a ce Murtala ya yi wa Barau aiki ya ci zabe. Ku tuna shi kan shi Murtala an cire masa lakar daga a fagen siyasa a sanadiyar rashin ba shi tikitin takarar gwamna da aka yi.