Farashin kayan abinci ya ƙara tashi a Najeriya a cikin watan Afrilu, daidai lokacin da tsadar ta ƙaru da har kashi 18.8%.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana haka bayan kammala binciken ƙididdigar watan Afrilu, a ranar Litinin.
NBS ta ce tsadar kayan abinci ya ƙara cillawa sama daga kashi 17.2 a cikin watan Maris, inda ya kai kashi 18.8 a cikin watan Afrilu.
Kayan abincin da NBS ta ce su na a sahun gaban ƙarin farashi sun haɗa da sarelak, kayan abinci, tumatir, dankalin Turawa, barasa, doya, kifi, nama, makamashi da kuma man girki.
Kayan abincin da ake nomawa a gona sun ƙara farashi a ƙididdigar shekara ɗaya, zuwa kashi 14.18 cikin watan Afrilu, 2022.
NBS ta ce gas ne ya fi tashin farashi sai mai, sutura da sauran kayayyaki.
Jihohin Da Su Ka Fi Fama Da Tsadar Kayan Abinci:
NBS ta ce a cikin watan Afrilu 2022, Jihar Kogi ce ta fi fuskantar tsadar kayan abinci da kashi 22.79. Sai jihar Kwara mai tashin farashin kayan abinci da kayan cefane zuwa kashi 21.56.
Yayin da Jihar Sokoto ke da kashi 14.85, jihar Kaduna ce ta fi dama-dama kashi 15.55.
Kusan shekaru biyar kenan ana fama da tsadar kayan abinci a Najeriya. Gwamnatin Buhari ta rufe kan iyakoki domin a hana shigo da shinkafa da wasu kayan masarufi daga ƙasashen waje.
Ta maida hankali wajen bunƙasa harkar noma. Sai dai kuma maimakon a samu sauƙin tsadar kayan abinci, a kullum sai farashin ke ƙara yin sama, abinci na neman ya gagari talaka.
Zuwa yanzu dai farashin kayan abinci ya nunka sau biyu bisa yadda Shugaba Buhari ya same shi kafin ya hau mulki.