Wani matafiyi da ya shaida harin da ƴan bindiga suka kai a titin Kaduna-Abuja ya bayyana wa BBC Hausa cewa lamarin ya auku ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammacin Talata.
Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda ke ajiye a kan ɓangaren zuwa Kaduna da ɓangaren dawowa da aka yi awon gaba da mutanen cikin waɗannan motoci.
Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗumbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki sai dai kuma ba su cimma maharan ba.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar abin inda ya ce jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan bindigar amma babu ƙididdiga ta mutanen da aka sace har yanzu, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Matafiya da dama sun dade suna kuka kan rashin jami’an tsaro da ba su a wannan titi a duk lokacin da tafiya ya kama mutum.
” Sau da sama za ka bi wannan hanya, maimakon aga jami’an tsaro na sintiri a hanyar akai akai ba zaka gani ba sai ka yi tafiya mai tsawo sai ka ga ƴan tsiraru a gefen hanya.
” Gwamnati ba ta kyauta ba ya kamata ace zuwa yanzu an gama da maganar ƴan bindiga a wannan hanya, amma ace abu yajlki ci ya ki cinyewa. Jirgin kasa, ba a tsira ba, mota a hanya ba a tsira ba, kullum sai ace an tira jami’an tsaro amma kuma babu gaskiya a ciki. ” In ji wani matafiyi da ya zanta da PREMIUM TIMES HAUSA.