Mummunan labarin da ya fito daga mahukuntan sojojin Najeriya ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna, inda su kashe soja shida a Jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne daidai lokacin da sojojin su ka yi ƙoƙarin kai wa ‘yan bindiga harin fatattakar su, yayin da maharan su ka dira garin Tati da ke cikin Ƙaramar Hukumar Takum.
Cikin wata takardar sanarwa ta cikin gida Sojojin Najeriya su ka fitar, har ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, Bataliyar Sojoji ta 93 da ke Takum, ta tabbatar da cewa zuwa yanzu ba a san halin da Kwamandan Bataliyar mai suna Laftanar Kanar E.S Okore ya ke ba.
Sanarwar ta ce mummunan harin ya faru a ranar 10 Ga Mayu, wajen ƙarfe 10 na safe.
Ta ƙara da cewa an yi gumurzu tsakanin sojojin da ‘yan bindiga, waɗanda sun nunka sojojin yawa.
Sai dai kuma sanarwar ta ce ba a kai ga tantance yawan waɗanda aka kashe a cikin ‘yan ba.
An kuma sanar cewa sojojin Najeriya a Donga kusa da ƙauyen Ananum sun kashe ‘yan bindiga biyu, yayin da wasu da dama su ka tsere da raunukan harbin bindigar da sojoji su ka yi masu a jikin su.
Sannan kuma Sojojin Najeriya sun ƙwato bindiga samfurin AK47 guda, albarusai da fistol ɗaya da tarkacen guru da layu da karhuna, har ma da kuɗi naira 15,120 a hannun ‘yan bindiga, lokacin da sojojin su ka yi artabu da ‘yan bindiga.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kuma yi awon-gaba da wani soja, lokacin da aka yi masa kwanton-ɓauna a kan hanyar sa ta komawa daga bakin aiki. Amma dai ya daga ƙarshe ya ƙwaci kan sa ya kuɓuta.
Sanarwar ta ce ana nan ana neman sojojin da ba a gani ba.
Discussion about this post