• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

    KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

    ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

    Thugs-attack-collation

    ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

    2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

    ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Daga Ƙarfe 11 Zuwa 12:30 Na Ranar Zaɓe

    INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

    ZAƁEN GWAMNA A KANO: Har ƙarfe 12 na ranar zaɓe ana ta raba wa talakawa taliya da atamfofi

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

TAKARAR SHUGABAN ƘASA A 2023: Kotu ta maida wa Godwin Emefiele hannun agogo baya

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 9, 2022
in Rahotanni
0
RA’AYIN PREMIUM TIMES: TAKARAR 2023: Ko dai Gwamnan CBN Emefiele ya fito ya yi magana, ko kuma ya yi murabus

Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da roƙon da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi mata a ranar Litinin, inda ya nemi ta amince ya fito takarar shugaban ƙasa ba tare da ya sauka daga kan muƙamin sa ba.

A cikin kwafen ƙarar wadda lauyan sa Mike Ozekhome ya shigar a yau Litinin, ya ce babu inda dokar Najeriya ta tilasta shi sauka daga mulki kafin tsayawa takara.

Emefiele ya maka Hukumar Zaɓe Ƙasa (INEC) a kotu, tare da Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami kotu.

Ya nemi kotu ta hana su haramta masa fitowa takarar da yayi niyyar yi.

Da ya ke yanke masa ƙwarya-ƙwaryan hukunci, Mai Shari’a Ahmed Mohammed ya ce ba zai iya hana INEC ko Antoni Janar hana Emefiele tsayawa takara ba, har sai ya gayyaci INEC da Antoni Janar, sun yi masa bayanin matsayar su tukunna.

Sannan kuma Mai Shari’a ya ce lauyan Emefiele ya yi kuskure, saboda bai aika wa INEC da Antoni Janar wasiƙa ko kwafen ƙarar da ya maka su a kotu ba.

Daga nan sai Mai Shari’a ya ɗage ƙarar zuwa 12 Ga Mayu, ranar da ya ce INEC da Antoni Janar za su bayyana a kotu, domin jin dalilan da ka iya sa su haramta takarar Emefiele, idan bai sauka daga muƙamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya ba.

Gwamnan CBN dai ya garzaya kotu a ranar Litinin, ya na neman damar tsayawa takara ba tare da ya sauka daga muƙamin sa ba.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya garzaya Babbar Kotun Tarayya, inda ya nemi kotu ta ba shi lasisin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, ba tare da ya sauka daga shugabancin CBN ba.

Emefiele ya shigar da ƙarar ta hannun lauyan da Mike Ozekhome, wanda a cikin ƙarar da ya shigar, ya yi wa kotu nunin cewa “babu inda dokar Najeriya ta haramta wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya tsayawa takara, matuƙar ya bayar da sanarwar sauka daga aiki kwanaki 30 kafin ranar zaɓen fidda-gwani.”

Ganin yadda ake ta ji-ta-ji-tar fitowar Emefiele takara tun a farkon wannan shekarar, PREMIUM TIMES ta buga ra’ayin ta cewa ko dai Emefiele ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan batun takarar sa, ko kuma ya yi murabus.

An ci gaba da yi wa Emefiele rubdugu, har wasu da dama ciki kuwa har da wasu gwamnonin ƙasar nan su ka yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige shi.

Yayin da a ranar Lahadi Emefiele ya ƙi karɓar tayin fam ɗin takara daga hannun ƙungiyar manoman shinkafa, Emefiele ya ce bai shirya fitowa ba tukunna. “Amma idan zan fito ɗin, zan sayi fam ne da kuɗaɗen da na riƙa yin asusu ina tarawa daga albashi na, a tsawon shekaru 35 da na yi ina aiki.”

PREMIUM TIMES ta yi dogon rubutu a ranar Lahadi, kwana ɗaya kafin Emefiele ya garzaya kotu.

Rubutun ya yi magana ne kan matsayin Emefiele da yadda APC ke cinikin fam ɗin takara.

Daga Fadar Shugaban Ƙasa har ofishin shugaban ƙaramar hukuma, kotu da sauran hukumomin gwamnati kowa ya san cewa ofishin Shugaban Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele bai amince wa duk mai riƙe da muƙamin ya tsoma hannu, ƙafa ko baki a sha’anin siyasa ba.

Amma kwatsam sai sunan Godwin Emefiele ya fara karaɗe soshiyal midiya, har ta kai ga wata ƙungiya ta manoma ta ce ta sai masa fam na takarar shugaban ƙasa na naira miliyan 100 cur.

Cikin watan Fabrairu PREMIUM TIMES ta bi sahun ‘ya Najeriya masu cewa ko dai Emefiele ya fito ya bayyana wa jama’a matsayin sa, ko kuma ya sauka daga shugabancin CBN.

Amma sai ya yi shiru, ya kauda kai daga kiraye-kirayen da ake yi masa. Hakan ya lokacin da labarin ƙungiyar Masu Noman Shinkafa ta ƙasa da abokan Emefiele aka ce sun haɗa kuɗi sun sai wa Emefiele fam na Naira miliyan 100.

Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Ƙasa Kan Rashawa (PACAC), Itse Sagay, ya bayyana cewa hankalin sa ya yi matuƙar tashi da ya ji cewa Emefiele na son fitowa takarar shugaban ƙasa.

Sagay ya ce idan ya yi haka ya karya dokar aiki.

Kiraye-kirayen Neman Emefiele Ya Yi Murabus:

Yayin da ake ci gaba da kiran Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sauka, shi ma Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya bi sahun masu kiran Emefiele ya ajiye aikin sa kawai. Ya ce lamarin zai gurgunta tattalin arzikin Najeriya. Kuma ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige shi.

Akeredolu ya buga hujja da Dokar Aikin CBN ta 1999 da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wadda ta haramta wa shugaban bankin tsoma baki cikin sha’anin siyasa.

Haka kuma jama’a da dama har da jam’iyyar PDP na ta kiraye-kirayen ko dai Emefiele ya sauka, ko kuma Buhari ya gaggauta tsige shi.

Wani mai rajin kare haƙƙin jama’a, Lauya Festus Ogun, shi kira ma ya yi bayan an tsige Emefiele, to EFCC ta fara gaggauta binciken irin gararumar da aka tafka a CBN a tsawon shekarun da Emefiele ya yi ya na mulki.

Ya nemi Buhari ya yi amfani da Sashe na 11(2) na Dokar CBN ya tsige Emefiele.

Ban Yanke Hukuncin Tsayawa Takara Ba Tukunna -Emefiele:

Daga ƙarshe dai ya yi magana cewa har yanzu bai yanke hukuncin tsayawa ba. Amma kuma ya gode wa masu neman ya tsaya ɗin.

Batun sayen fam kuma ya ce idan ya yi shawarar tsayawa, to shi da kan sa zai yi amfani da kuɗaɗen albashin sa da ya ke yin asusu ya na tarawa a tsawon shekaru 35 ya na aiki, ya sayi fam da su.

Zuwa yanzu dai sama da mutum 30 ke neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC. A cikin su kuma mutum 25 sun sayi fam na Naira miliyan 100 kowanen su.

Cikin watan Fabrairu PREMIUM TIMES ta buga ra’ayin ta cewa ko dai Gwamnan CBN Emefiele ya fito ya yi magana kan batun takarar sa ta shugaban ƙasa a 2023, ko kuma ya yi murabus.

Wannan ya nuna cewa an daɗe kenan ana ƙishin-ƙishin ɗin fitowar sa takarar.

A ra’ayin wa wannan jarida ta buga a lokacin, ta ce, a duk lokacin da batun zaɓen shugaban ƙasa ya kunno kai tun daga bayan samun ‘yanci har zuwa yau, har ɓarkewar Yaƙin Basasa, a kullum tashin hankalin da ke lulluɓe ruɗanin zaɓen sai ƙara muni ya ke yi.

Ta shiyyoyi da yankuna da dama tantagaryar ‘yan takifen maɓarnata da makasa ne sun tsare ƙofar shiga farfajiyar dimokraɗiyyar mu. A mafi yawan yankunan Arewa har zuwa Kudu, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ‘yan takife ne ke amfani da muggan makamai su na ƙoƙarin ganin sai sun kassara ƙasar nan. A lokaci ɗaya kuma su na ƙoƙarin sai sun durƙusar da tattalin arzikin ƙasar nan.

Ko ta ina a cikin ƙasar nan ana fama da rayuwar ƙunci da tsada. Ga matsalar rashin aikin yi sai ƙara ta’azzara ta ke yi. Fatara da talauci sai ƙara katutu su ke yi. Ƙarin abin takaici shi ne yadda farashin kusan komai ke ƙara hauhawa a ƙasar nan.

Romon-kunnen da aka yi kwanan nan aka ce malejin tattalin arziki ya cilla sama, ya ɗan bunƙasa, to cirawa saman da ya yi ba zai iya sa tatttalin arzikin ya yi tashi ba, kai ko gwauron numfashi ma ba zai iya yi ba.

Daɗin daɗawa kuma a daidai wannan lokaci da ake ta kiki-kaka da ƙadabolon yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa fitar da kitse daga wuta, balle a samu rangwamen da ta yi alƙawarin samarwa, an fara tunanin wanda zai gaji kujerar shugaban Najeriya a shekara mai zuwa. Daga cikin masu hanƙoron ganin sun hau kujerar, wani mutum ɗaya da ya ɗauki hankalin wannan jarida, shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Yayin da wasu ‘yan gararuma su ka fara ɓaɓatu da hayagagar cewa Emefiele ne ya cancanci zama shugaban ƙasa, saboda zai iya warware ƙabli da ba’adin da duk wata rabkanuwar da ta yi wa Najeriya da tattalin arzikin ta dabaibayi, PREMIUM TIMES na ganin cewa tatsuniya ce kawai ake yi, domin duk wata matsala da cukurkuɗewar da tattalin arzikin Najeriya ya yi, Godwin Emefiele ne ɗin nan ne dai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, tun daga 2014 har zuwa yau.

Mafarki ne kawai ake yi da soki-burutsu, a ce wai mutumin da ya kai darajar naira cikin kwazazabon ramin da ta kasa fita, kuma a ce shi ne zai gyara Najeriya.

Yayin da Emefiele ya karya Dokar Aikin CBN, ya bi ruɗin jagaliyar ‘yan siyasa a matsayin sa na Gwamnan CBN, lamarin kamar akwai lauje cikin naɗi. Bai kamata Emefiele ya ci gaba da zama gwamnan CBN ba. Kuma bai kamata a kare shi ba ya ci gaba da zama gwamna, kuma ya na siyasa.

Idan Emefiele na so ya fito takarar siyasa don neman kowane muƙami, hankali da tunani da ya kamata sun nuna bai kamata ya ci gaba da riƙe muƙamin sa na Gwamnan CBN ba. Sannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa har yau bai nesanta kan sa daga masu haƙilo da hanƙoron masu neman ya zama shugaban ƙasa ba.

A kan haka ne PREMIUM TIMES ke yin kira ga Emefiele ya girmama muƙami da kujerar Gwamnan CBN, ya sauka daga muƙamin, ya je ya yi siyasar sa. Idan kuma babu ruwan sa da batun takarar sa, to ya fito ya nesanta kan sa, su daina, a wuce wurin.

PREMIUM TIMES ta haƙƙaƙe cewa muddin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito ya fara neman kujerar shugaban ƙasa tun ya na kan aikin sa, to tabbas martaba da ƙimar wannan banki wanda shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya, ta zube ƙasa warwas.

Dama kuma tun za zaɓen 2015 aka fara nuna damuwar cewa CBN ya shiga hidimar zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen, da ma wasu zaɓukan baya.

Tags: AbujaCBNGodwin EmiefileHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

RUGUJEWAR BENE A LEGAS: Minista Sadiya na so a tilasta bin ƙa’idojin gine-gine

Next Post

TABARBAREWAR TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 78 a makon jiya a Najeriya

Next Post
Neman aure ya yi sanadiyyar mutuwar Nabajallah, kasurgumin dan bindiga a Katsina

TABARBAREWAR TSARO: 'Yan bindiga sun kashe mutum 78 a makon jiya a Najeriya

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • ƊAN HAKIN DA KA RAINA: Yadda Lawal Dare ya kakkaɓo ‘jiragen yaƙin’ Matawalle, Yari, Shinkafi da Yarima a Zamfara
  • ZAƁEN GWAMNONIN 2023: Gwamnonin da su ka kammala wa’adi da zaɓaɓɓun da za su gaje su
  • ANA WATA GA WATA: APC ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen gwamnan Bauchi, ta ce an ɗibga maguɗi
  • TARABA TA JUYE: Kefas na PDP ya zama zaɓaɓɓen gwamna, NNPP ta yi bazata
  • ZAƁEN GWAMNAN BARNO: Yadda Zulum ya zunduma Jajari na PDP rijiya, ya bi ya danne shi da ƙuri’u 545,000

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.