Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya fara tunanin wanda zai ɗauka domin yi masa takarar mataimaki.
Sai dai kuma majiya ta tabbatar da cewa Atiku na ganawa da Shugaban APC Iyorchia Ayu, domin ya ɗauki mataimaki daga cikin gwamnoni biyu na Kudu maso Kudu.
An ce hankalin sa ya tafi a kan Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta da kuma Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom.
Sai dai kuma waɗanda ba su iya ji da gani su yi shiru na cewa Atiku ya fi so ya ɗauki Ifeanyi Okowa saboda shi kaɗai ne Gwamnan Kudu maso Kudu da ya sa wakilan sa su ka jibga masa ƙuri’un su.
Shi kuma Udom Emmanuel na Akwa Ibom, ya tsaya takara amma ya samu ƙuri’u 31 kacal.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin irin kakkausan kalaman da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yi, inda ya ragargaji zaɓen fidda-gwanin PDP.
Ya ce ya so ya hargitsa taron saboda cin mutuncin da aka yi masa. Amma ya kai zuciya nesa, don kada ya gurgunta PDP ɗin ce baki ɗaya.
A takarar 2019 dai Atiku ya ɗauki tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi.
“Da na ga damar tayar da rigima, da na hargitsa zaɓen fidda-gwani, kowa ya rasa.”
Gwamna Nyesom Wike ya zargi Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da wani Gwamnan Kudu maso Kudu da cin amanar sa da kuma shirya masa maƙarƙashiya a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa, wanda aka yi a ranar Asabar a Abuja.
Wike ya yi wannan kakkausan kalamai ne a Fatakwal, wurin gangamin da aka shirya domin tarbar sa, bayan ya koma gida daga wurin zaɓen fidda-gwanin da ya samu ƙuri’u 237. Atiku Abubakar ne ya kayar da shi, bayan ya samu ƙuri’u 371. Bukola Saraki ya samu ƙuri’u 70, yayin da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom ya samu ƙuri’u 31.
Wike ya yi zafafan kalamai ne sakamakon maƙarƙashiyar da ya ce an shirya masa a wurin taron, yadda shugabannin jam’iyyar PDP su ka bari Tambuwal ya janye daga takara, alhali a lokacin bai kamata ya janye ba, saboda lokacin janyewar ta sa ya wuce.
A bayanin Wike, ya ce Kwamitin Tantance ‘Yan Takara a zalunce shi, domin ya bayar da dama ga Tambuwal ya yi magana sau biyu. Hakan kuma a cewar Wike, an karya ƙa’idar zaɓen fidda-gwani.
“Da na so tayar da fitina, da sai na tashi daga inda na ke na je na ce ban yarda a ci gaba da taron ba. Saboda an bai wa Tambuwal lokacin da ya zarce na kowa, kuma na ƙa’ida, har ya yi dogon jawabin cewa ya janye, ya goyi bayan Atiku Abubakar.
“Amma saboda ba na son tayar da fitinar da za ta hargitsa PDP baki ɗaya, sai na haƙura don a zauna lafiya.
Wike dai ya yi raga-raga da shugabannin PDP, ya ce kwata-kwata babu adalci a lamarin su.
Da ya koma kan Gwamnonin Kudu maso Kudu, Wike ya ce wanda ya ci amanar sa bai rage shi da komai ba, amanar kan sa ya ci.
Bisa alama ya na magana ne kan Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta, wanda wakilan zaɓen ‘yan takarar jihar sa su ka zaɓi Atiku, maimakon Wike, kamar yadda shi Okowa ɗin ya sha cewa ɗan Kudu za su zaɓa.
“Na taya Atiku murna don a tafi tare, kuma jam’iyya ta kauce wa ruɗani. Na sanar da shi da ya zo gida na a Abuja cewa na ga wasu tarkacen gwamnoni da ‘yan miya-ta-yi-zaƙi na bin ka ɗuuu. To waɗannan duk fanko ne, ba su da mutane. Ni ke da mutane, kuma ta tabbatar zaɓe ya nuna haƙa.”
Masu nazarin siyasa na ganin cewa magoya bayan Tambuwal da na Gwamnan Delta ne su ka ƙara wa Atiku yawan ƙuri’u, har ya kayar da Wike.”
Gwamna Wike ya ce tunda Kudu ba su da haɗin kai, daga yau kada wani maras kunya ya fito ya ce Arewa ta danne su, domin su ne su ka danne kan su.
Idan ba a manta ba, Wike ya goyi bayan Tambuwal a zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP.
Discussion about this post