Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki za ta tayar da batun yiwuwar bin tsarin karɓa-karɓa bayan kammala tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa.
Adamu ya yi wannan bayani a wata tattaunawa da ya yi da wasu kafafen yaɗa labarai na Hausa a ranar Laraba da dare.
Adamu ya ce za a tantance dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa daidai yadda tsarin da ƙa’idar zaɓen 2023 ya shimfiɗa.
INEC ta amince da ƙa’idoji uku na fitar da ɗan takara, waɗanda su ka haɗa da zaɓen kaɗa ƙuri’a, ‘yar-tinƙe, wato ƙato-bayan-ƙato da kuma cimma yarjejeniyar tsaida ɗan takarar bisa amincewar sauran masu takarar.
Da ya ke magana kan tsarin karɓa-karɓa, Adamu ya ce har yanzu ba a kai ga batun ba tukunna, idan ma har za a yi. Ya ce sai bayan kammala tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC ɗin sannan a bijiro da maganar.
“Ai kun ga har yanzu ba mu fitar da ɗan takarar mu ba tukunna na shugaban ƙasa. Sai bayan mun yi tantancewa sannan za mu nemi mafitar yadda za a fito da ɗan takarar mu.
“Mu na da ‘yan takarar shugaban ƙasa daga sassan ƙasar nan daban-daban. Sai mun kai ga wurin fitar da ɗan takara sannan za mu san mafitar yadda za mu tsayar da ɗan takara ɗaya daga cikin su.” Inji Adamu.
Da aka yi masa maganar yawan ‘yan takarar a APC, Adamu ya ce ai ba za a hana wa duk wani ɗan jam’iyyar ‘yancin fitowa takarar shugaban ƙasa ba.
Batun zargin yadda ake raba wa wakilan zaɓen ‘yan takara kuɗi kuwa, Adamu ya ce shi dai ba shi da wata shaidar afkuwar haka.
Ya ce duk da irin tsangwamar da wasu ke yi wa APC, har yanzu babu wata jam’iyya mai ƙarfin iya cin zaɓe kamar APC ɗin.