Akalla ƴan jam’iyyar PDP 9 dake majalisar dokokin jihar Kano ne suka canja sheka zuwa jam’iyya mai alamar kayan marmari, jam’iyyar NNPP.
Dukkan su ƴan majalisan suna tare ne da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso wanda a kwanakin baya ya koma jam’iyyar sannan kuma tuni har ya siya fom ɗin takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar.
Waɗanda suka koma sun haɗa da:
Isyaku Ali Danja (Gezawa), Umar Musa Gama (Nassarawa), Aminu Sa’adu Ungogo (Ungogo), Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa (Dala) da Tukur Muhammad (Fagge).
Sauran sun haɗa Mu’azzam El-Yakub (Dawakin Kudu), Garba Shehu Fammar (Kibiya), Abubakar Uba Galadima (Bebeji) and Mudassir Ibrahim Zawaciki (Kumbotso).
Discussion about this post