Tarzoma ta ɓarke a Sokoto, kwana ɗaya bayan kisan ɗalibar Kwalejin Shehu Shagari, wadda hasalallun matasa su ka kashe, bayan ta yi kalaman zagi kan Annabi (SAW).
An sa dokar-ta-ɓaci a Sokoto, bayan hasalallun matasa sun kai wa Fadar Sarkin Musulmi farmaki, yayin da su ke zanga-zangar neman a saki mutanen da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta ce an kama saboda zargin su da ake yi da kisan Deborah.
Masu zanga-zangar dai sun yi dafifi a Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, inda su ka riƙa antaya jifa da duwatsu a gidan.
Wasu masu zanga-zangar sun yi dafifi a ƙofar shiga Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto, su ma su na neman a saki waɗanda aka ce an kama ɗin.
Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya ƙaƙaba dokar hana walwala tsawon sa’o’i 24, bayan da zanga-zanga ta ɓarke a Sokoto, a ranar Asabar.
Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Tambuwal, Mohammed Bello ya fitar a shafin sa na Facebook, ya ce, “an sa dokar ce a cikin Sokoto da kewaye, domin tabbatar da zaman lafiya, biyo bayan zanga-zangar da ta ɓarke, kwana ɗaya bayan kiran wata ɗaliba a Kwalejin Shehu Shagari, wadda aka yi zargin ta yi ɓatanci ga Annabi (SAW).”
“Gwamna Tambuwal ya sa dokar a bisa ikon da tsarin mulki ya ba shi a ƙarƙashin Sashe na 176(2) na Dokar Gwamnatin Tarayyar Najeriya. Da kuma Dokar Jihar Sokoto ta Sashe na 15, Dokar Tabbatar da Zaman Lafiya.
“A kan haka ne aka sa dokar hana shiga da fita da walwala daga safe zuwa safe, wato sa’o’i 24.”
PREMIUM TIMES Hausa ta gano cewa matasan sun fusata ne da kalaman da Sarkin Musulmi ya yi, inda ya yi tir da kisan da aka yi wa Deborah.
Sanarwar da aka fitar daga Sarkin Musulmi tun a ranar Juma’a dai ta fusata Musulmi da dama.
Haka malamai daban-daban daga ɓangarori daban-daban sun riƙa goyon bayan kisan, tare da sukar Sarkin Musulmi da duk wani wanda ya nuna rashin goyon bayan kisan Deborah da aka yi a cikin kwalejin.
Bayan kisan ɗalibar ne ‘yan sanda su ka bayyana cewa sun kama mutum biyu masu hannu wajen kisan ta da ake zargin sun yi.
Wakilin mu ya nemi jin ta bakin Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, amma hakan bai samu ba.
Tun da farko dai an fara zanga-zangar cikin lumana, amma daga baya ta koma tarzoma, inda jami’an tsaro ta kai sun yi amfani da barkonon-tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Haka nan wani babban malami a Sokoto ya yi bidiyon da ya nuna cewa lallai a saki dukkan waɗanda aka kama da zargin kisan Deborah Samuel.