Ta tabbata a wannan karon ma Gwamnan Jigawa mai barin gado zai yi takarar shugabancin kasar Nijeriya, amma fa akasarin takarkarin da wayanda ya gada suka yi a baya tamkar taka-kara ne, kusan cewar babu wani tasiri da takarar tayi, face a kira su da sun taba takara. Shin wannan takarar ma ta gwamna Badaru zata zamanto takara ko kuma tayi tasirin da dole sai an dama dashi a fagen siysar kasar nan? Ko kuma ita ma zata zamanto taka-kara?
A siyasar bana, Jama’iyar APC mai mulki tazo da wani sabon salo wanda kawai lokaci ne zai nuna yadda tafiyar da dosa, musamma ma wajen fidda dan takarar ta a zaben 2023, ganin irin yadda kowane launin mutune ma ke kokuwar sayen tikitin takarar wannan kujera. Amma duka wannan ba wani abin mamaki bane bisa yadda jamaíyar ta dau tsawan lokaci cikin rigingimu da kuma rabuwa kai tskanin manyan jagorotinta.
Za kuma a iya kara cewa wannan ruruwa na da alaka da komabayan da aka samu wajen samun ingantaccen mulkin dimokaradiyya, ta yadda neman mulki a wajen jagorori ya zarta neman samawa kasa makoma da ci gaban ta.
Jihar Jigawa, ganin da akewa Jaha irin ta Jigawa a tsakanin takororin ta na Nijeriya, tana da ga cikin komabayan jihohi a Nijeriyana (wato jaha ta cika dabi’u, mutane jumulda irin ta katafatanin Nijeriya). To in kuwa hakane, kwarewa da mutum ya samu a matsayin sa na gwamna ya wadatu ya iya jagorancin Nijeriya? Shin kuma sauran yan Nijeriya zasu iya gamsuwa da cewa gwamnoni irin na su Jigawa kan iya jagorancin wannan kasa, ganin irin gwamatsayya, banbance-banbance da kuma rigingimu da wannan kasa ke fama da ita tun lokacin da kasar nan ta zama Nijeriya?
Manazartan siyasar Nijeriya a baya sunyi nuni da irin kalubalen da tsohon shugaban kasa Marigayi Umaru Yar’adua ya samu na gaza kamo kan zaren Nijeriya a farkon mulkin sa, ya hada da karancin kwarewar sa akan fahimtar babbar kasa irin Nijeriya, har rashin lafiya ta iske masa, shi ma kansa Jonathan irin wannan rashin kwarewa ya jefa shi ramin da ya kawar dashi a kan mulkin kasar a shekara ta 2015.
Amma duk da haka akan iya cewa kowa akwai irin tashi baiwar, duba kuma da chanje-chanje da aka samu na mu’amala a tsakanin yan kasar a yau, ko irin mu’amalar gwamna Badaru da kuma jagorancin da yakeyi a matakin tarayya kan iya banbanta shi da takwarorin sa.
Jonathon da Badaru, shin da gaske ne takarar Gwamna Badaru na da alaka da takarar tsohon shugaban kasa Ebele Jonathan? Kamar yadda labarai ke yawo a kafafen yada labarai cewa Jonathon ne ya bawa Badaru kudi ya saya musu Form din takara a APC, kawai anyi amfani da kungiyar Fulani ne cewar su suka saya wa Jonothan Form, amma koma yaya maganar take ba a cewa ga rami a wurin da babu ramin.
Wannan batu da alkar wasu gwamnonin APC da Janathon, a bisa nazari na siyasa kan iya yin kamantacceniya da gaskiya, yayin da akayi tankade da reraya na abin da ya faru a jahar Bayelsa yayin zaben gwamnan jahar wanda shi Badarun ne ya jagoranci ‘yan Jamaíyyar APC har sukayi nasara, saidai daga baya PDP ta kayar da APC a kotu. Harila yau in aka yi la’akari da yadda gwamnonin jama’iyar APC kansu ya rabu tun kafin a yi zaben shugabnnin jama’iyar a baya, wannan kan iya gina irin wanna alaka ta siyasa.
Badaru da Gwamnatin Buhari, tabbas nazari ya nuna cewa, tsare-tsaren da Gwamna Badaru ya bullo da su a jahar sa, musamman ma na tattalin arziki, noma da tsantsani yayi kama da irin tsarin gwamnatin Buhari, watakilla hakan yasa ya kasance gwamnan da yafi kusantuwa da gudanarwar gwamnati da kuma amincewar da Shugaba Buhari yake yi masa.
Gwamna Badaru ne ke shugabantar kwamitin Shugaban Kasa na samar da Takin Zamani, wanda alkaluma suka nuna an sami gagarimin nasara. Badaru ne ke Shugabantar Kwamittin Shugaban Kasa na samawa Nijeriya kudin shiga ba ta hanyar mayin fetur, shima alkalima sun nuna irin dunbin nasarorin da aka samu, Badaru yayi jagorancin a wasu manyan al’amuran da suka shafi jamaíyyar APC dama kasa. Wannan kan iya nuna cewa yana da masaniyar da zata taimakeshi jagorancin Nijeriya.
Tuntuba da yada manufofin Gwamna Badaru, wai shin kawai aiyana takara ko sayen tikitin takara ne yin takara? Tabbas duk masu neman takara kan yi yawo wajen tuntubar abokan siyasa, dattawa da shugabanni, kuma sukan tallatawa da ilimantar da masu zabe irin manufofin su, nagartar su, kwarewar su domin samun nasara.
Da dukkan alamu, nazari ya nunna takarar Gwamna Badaru na da karancin tallatawa da ma tuntuba, duka da kasancewar a tsakanin shekara 2015 kawo yau,irin gwagwarmayar da yayi a siyasar Nijeriya da kuma tsare-tsaren da ya kawo a jahar sa na bunkasa tattallin arziki, noma, sun wadatu a ja hankalin masu zabe su dawo kan Gwamna Badaru.
A karshe, mu fatan mu wannan takara a bana ta zama takara ba taka-kara ba, domin tabbas taka-kara kan mayar da Dan Siyasa baya, tabbas yan Jigawa a yau suna da abin fada a takarar bana in har sun san yadda zasu fada, kuma su kan iya yin nasara in har sun fahimci hanyar yin nasarar.
alhajilallah@gmail.com