A cikin wannan mako ne shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Yahaya Abdullahi ya fito takaran gwamnan jihar Kebbi a karkashin inuwar jami’ayya APC.
Abdullahi wanda ke wakiltar Kebbi ta Arewa a majalisar na daya daga cikin shugabannin bangaren jami’yyar APC dake adawa da gwamnan jihar Atiku Bagudu.
Mai taikamawa gwamna Bagudu kan harkokin yada labarai Zaidu Bala ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.
Abdullahi ya bi sawun Atone-janar kuma ministan Shari’a Abubakar Malami domin fafatawa a takarar kujerar gwamnan jihar Kebbi.
Tsohon ɗan majalisan wakilai sannan dan uwan gwamna Bagudu, Bello Bagudu na daga cikin waɗanda ke kan gaba wajen yin adawa da zaɓin gwamnan sannan kuma ke mara wa sannan kuma da shi aka je aka sayi fom ɗin takarar.
A jihar Kebbi jami’yyar APC ta rabu biyu inda ɓangare ɗaya na goyan bayan Atiku Bagudu ne, gwamnan jihar dake mara wa Malami baya, shi kuma bangaren Tsohon gwamnan jihar Adamu Ailero na mara wa Abdullahi baya kuma suna adawa da zaɓin Malami.
Aliero wanda ke wakiltar Kebbi ta Tsakiya na goyan bayan Abdullahi sannan Bagudu na goyon bayan Malami a takarar gwamnan jihar.
Bagudu ya siya fom din takarar sanata na Kebbi ta Tsakiya kujerar da Ailero ke kai.