Jam’iyyar APC ta bayyana farin cikin ta ganin yadda Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya faɗi zaɓen fidda-gwanin PDP na ‘yan takarar shugaban ƙasa.
APC Reshen Jihar Ribas ce ta nuna farin cikin, ta na mai cewa Wike ya faɗi zaɓe ne saboda addu’ar ma’aikata, ‘yan fansho da marasa galihun jihar da ya hana albashi da haƙƙoƙin su ta yi tasiri a kan sa.
Sakataren APC Chris Finebone ne ya nuna farin cikin a Abuja a wata ganawa da ya yi da manema labarai.
“Faɗuwa zaɓen Wike ta zo daidai lokacin da ya bar Jihar Ribas a cikin halin ƙaƙanikayi, lokacin da ya ke kwasar dukiyar jihar ya na bindiga da su da sunan takarar neman shugaban ƙasa da kuma halin watsi da tafiyar da Gwamantin Ribas cikin halin ba ruwa na da Wike ya yi.
“Ubangiji ya amsa addu’ar al’ummar waɗanda su ka riƙa shaƙa masa addu’ar fatan rashin nasara. Ya riƙe masu albashi ya riƙe masu kuɗaɗen fansho. Shekaru bakwai kenan bai yi wa ma’aikata ƙarin girma ba. Ya riƙe kuɗaɗen ‘yan fansho da na gararuti.
“Wike ya yi kunnen-uwar-shegu ya ƙi sauraren kiraye-kirayen ƙungiyoyin da su ka riƙa ba shi shawara cewa kada ya shiga neman takarar shugaban ƙasa. Saboda ya shiga ɗin ya bar babban birnin jihar a lalace, sai tulin ƙazanta da bola ko’ina.
“Cututtuka sun yi wa jama’a rubdugu sannan kuma tiƙa-tiƙan ɓeraye sai walwala su ke yi a Fatakwal.”
APC ta ce tunda ya sha kaye a zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP, ya zama wajibi ya maida hankalin sa wajen kula da Jihar Ribas, ko kuma ya yi murabus kawai, wanda ya fi shi kishi ya karɓi ragamar gwamnan jihar.
Finebone ya ce ya yi mamakin da har Wike ya yi tunanin fitowa takarar shugaban ƙasa, alhali bai san komai ba game da yadda ake bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Discussion about this post