Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa na APC ya tantance ‘yan takara 12 a ranar Litinin.
Kwamitin wanda ke ƙarƙashin shugabancin tsohon Shugaban APC na Ƙasa, John Oyegun, ya ware ranakun Litinin da Talata domin aikin tantancewar da ake yi a babban ɗakin taron otal ɗin Transcorp Hilton, Abuja.
Waɗanda aka rigaya aka tantance sun haɗa da:
Emeka Nwajiuba, Davida Umahi, Felix Nicholas, Ibikunle Amosun, Gwamna Badaru Abubakar, Sanata Ajayi Borroffice da Ken Nnamani.
Sauran sun haɗa da Uju Ken-Ohaneye, Rotimi Amaechi, Ahmed Yerima da Bola Tinubu.
Dukkan su dai kowane ya bayyana irin tasirin sa da cancantar sa da kuma irin ci gaban da ya ce zai samar wa ƙasa.
An tantance Tinubu a lokacin da wata ƙungiya ta rubuta takardar rashin cancantar sa fitowa takarar shugaban ƙasa, domin a cewar ƙungiyar, ya na da takardun shaida waɗanda ba su cancanci tsayawar sa takarar ba.
A yau Talata ne kuma za a tantance sauran, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, Rochas Okorocha da sauran su.
Sai dai kuma ba a sani ba ko Babbar Kotun Tarayya za ta bayar da belin Okorocha kafin a kai ga lokacin tantance shi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ba a ga gilmawar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a wurin tantancewar ba a ranar Litinin.
Jonathan ya ƙaurace wa dandalin tantance ‘yan takarar APC.
Jam’iyyar APC mai mulki ta fara aikin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa, bayan tsaiko na makonni biyu da aka samu.
A yanzu haka dai ana tantancewar a otal ɗin Hilton, Abuja.
Tun da farko dai an tsara za a yi aikin tantancewar a ranakun 14-15 Ga Mayu, amma sai aka ɗaga zuwa ranar 23 Ga Mayu.
Daga nan kuma an sake ɗagawa zuwa 29 da 30 Ga Mayu, yayin da kuma aka ɗaya Gangamin Zaɓen Takarar Shugaban Ƙasa zuwa 6 zuwa 8 Ga Mayu.
Duk da an hana ‘yan jarida shiga zauren tantancewar, an ruwaito cewa za a tantance ‘yan takara ne su 23, ciki har da Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da kuma Rotimi Amaechi.
Yayin da Jonathan ya ƙi karɓar fam ɗin da wata ƙungiya ta ce ta sai masa, hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke shi ne Jonathan na da ‘yancin sake tsayawa takara a zaɓen 2023.
Sai dai kuma yayin da ake tantance ‘yan takarar APC a yau Litinin a Abuja, har yanzu ba a ga wulgawa ko giftawar Jonathan a wurin tantancewar ba.
A halin yanzu dai Jonathan ya na ƙasar Italiya wurin taron Ƙungiyar haɗin guiwar Afrika da Gabas ta Tsakiya.
Discussion about this post