Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta na tunanin kwashe dukkan wasu muhimman takardu da bayanan zaɓe daga Babban Bankin Najeriya (CBN).
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja.
Bayanin na Yakubu na da alaƙa da wata tambaya da aka yi masa, dangane da shigar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, har ya ke yunƙurin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Duk da dai har yau bai fito ya ce zai tsaya takara ba, amma ana ta kiraye-kirayen ya fito takara. A gefe ɗaya ana kuma ragargazar sa, ganin yadda ya shiga APC alhali ya na kan muƙamin da ya kamata a ce ya sauka.
Sannan kuma Emefiele ya maka Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da Ministan Shari’a Abubakar Malami a kotu, ya na ƙalubalantar su cewa kada su hana shi fitowa takara don bai sauka daga shugabancin CBN ba.
Wani gungun mutanen da su ka kira kan su Ƙungiyar Manoman Najeriya ne su ka sayi fam ɗin takarar shugabancin Emefiele na naira mijiyan 100.
Shi kuwa Shugaban INEC cewa ya yi “INEC ta fara tunanin kwashe muhimman takardun zaɓe da ke adane a cikin CBN.
“A yanzu da mu ke maganar nan, Daraktan Shigar da Ƙararraki na INEC ya na kotu. Ya je ne domin kotu ta ji ta bakin INEC kan wata ƙara da aka shigar. To a na mu ɓangaren ba mu son tsoma baki kan harkokin da ke gaban kotu.
“Amma mun fara maganar shin a ina za mu kai muhimman kayan zaɓe idan mun kwashe su daga CBN.”
Shigar Emefiele cikin APC ya ƙara kawo ruɗani, har ta kai ya na cikin manyan muƙarraban gwamnati da Buhari ya rubuta wa wasiƙar cewa duk mai don shiga takarar wani muƙamin siyasa, to kada su wuce ranar 16 Ga Mayu ba tare da sun yi murabus daga muƙaman ba.
A ranar Alhamis kuma Gwamnan na CBN ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara fadar Shugaban Ƙasa.
Ya shaida wa manema labarai cewa batun yamaɗiɗin da ake yi da shi, tare da neman a tsige shi, dariya su ke ba shi.