‘Yan takarar shugaban ƙasa musamman daga ɓangaren PDP, sun maida zuwa kai ziyara gidan iyalan marigayi Umaru ‘Yar’Adua tamkar wani shikashikan da idan ba su je ba, to zuwan su Katsina bai tabbata ba, ko ba a karɓe su ba.
Daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa shida, ɗaya ne kawai bai samu zuwa ba. Hatta Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo da ke PDP, sai da ya je ya gaishe da mahaifiyar tsohon Shugaban Ƙasa, Umaru ‘Yar’Adua.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ne kaɗai bai je ya gaishe da Hajiya Dada Aya Yar’Adua ba, wato mahaifiyar Umaru ‘Yar’Adua da Shehu ‘Yar’Adua a makon da ya gabata.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Udom Emmanuel na Akwa Ibom da Peter Obi, Tsohon Gwamnan Anambra, duk sun ziyarci gyatumar.
Shi dama Atiku Abubakar ya saba zuwa gaishe ta a duk lokacin da ya ziyarci Katsina. Musamman saboda Shehu Yar’adua ubangidan sa ne.
Atiku ɗin ya ce gidan ‘Yar’Adua tamkar gidan su ne, saboda kusancin sa da Marigayi Shehu ‘Yar’Adua.
Atiku ya ce duk lokacin da ya je Katsina, idan bai je gidan ya gaishe da Hajiya Dada ba, to ziyarar sa ba ta cika ba.
“Na zo kuma na yi farin ciki da na ga Dada lafiyar ta ƙalau.” Inji Atiku.
Kafin Shehu ‘Yar-Adua ya zama Mataimakin Shugaba Yakubu Gowon, iyalan ‘Yar’Adua sun fara ginuwa ne tun a Jamhuriya ta farko, lokacin da Musa Tafidan Katsina ya zama Ministan Harkokin Legas. Musa ya zama Matawallen Katsina.
Da Musa da Sarkin Katsina na lokacin, Usman Nagogo ‘yan uwan juna ne. Su na daga sahun farko na manyan ‘yan bokon Katsina.
Musa malamin Turanci ne kuma ya yi karatu a Babbar Kwalejin Katsina (Katsina Higher College) a zamanin Turawan mulki.
Dalilin Kai Ziyara: Ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon Shugaban Ƙasa Umaru ‘Yar’Adua mai suna Ibrahim ‘Yar’Adua, tasirin da iyalan su su ka dasa kuma ya kafu a siyasar Najeriya ne ya sa har yanzu masu neman takarar shugaban ƙasa ke kai ziyara gidan su.
Ya kuma nuna jin daɗin sa, tare da nuna irin yadda Shehu ya cicciɓa manyan ‘yan siyasa har su ka zama wani abu a can baya da kuma yanzu.
Shehu ya yi takarar shugabancin ƙasa a baya ƙarƙashin rusasshiyar jam’iyyar SDP.
Umaru ya yi Gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007. Kuma ya yi Shugaban Ƙasa daga 2007 zuwa 2010.
Ya ci gaba da cewa Goodluck Jonathan ma an ɗauke shi kamar ɗan gidan.