Ɗimbin ma’aikatan jihar Kano sun wayi gari safiyar Sallah su na fesa wa Gwamna Abdullahi Ganduje zafafan kalamai, har da tofin Allah-wadai da Allah-ya-isa, ganin yadda ya ƙi biyan su albashin watan Afrilu domin su yi abincin Sallah a wadace, duk kuwa da cewa Sallar ta zo a ƙarshen wata.
Da yawa na jin haushin yadda Ganduje ya lula Saudiyya domin yin Umrah, ya bar su babu albashi.
Wakilin mu ya lura da yawan ma’aikata a cikin unguwanni su na kukan rashin biyan albashi, tun a ranar jajibiri.
Ɗimbin ma’aikatan sun shafe ranar Lahadi, kwana ɗaya kafin Sallah su na sauraren waya domin su ji ‘alat’ na shigar albashi a asusun su na banki, amma shiru.
“Ba don na je wurin wani ubangida cikin dare ya ba ni naira 20,000 ba, to da ko abincin Sallah ba za a iya girkawa a gida na ba.” Haka Malam Bashir ya shaida wa wakilin mu bayan an tashi daga Sallar Tarawi Idi.
Shi kuwa Hamisu ya shaida wa wakilin mu cewa, “Saboda Allah ya gwamna zai tafi Saudiyya ya yi ta bindiga da kuɗi a can, amma ya hana mu albashi a ƙarshen watan Sallah? Na san dai ba kyauta ya ke zaune a can ba, kuɗi ya ke kashewa.”
Wakilin mu ya lura a wannan sallar ba a yi hada-hada da walkajamin rabon naman dabbobi na watanda ko naman kaji da yawancin ƙananan ma’aikatan Kano ba.
“Ai dama ƙaramin ma’aikaci tsaicon biyan albashi ke shafa. Amma babban ma’aikaci abin bai shafe shi ba. Saboda shi dama aljihun su ai ba zai taɓa rabuwa da nauyi ba.” Inji wani da ba ya so a ambaci sunan sa.
Sai dai kuma da yawan ma’aikatan da ke raba ƙafa su na wasu sana’o’i ko kasuwanci, rashin biyan albashi bai shafe su ba.
Wani da ya shaida wa wakilin mu cewa baya ga aikin gwamnati da ya ke yi, ya na kuma koyarwa a Islamiyya ana biyan sa. Kuma ya na ladanci a wani masallacin da ke cikin jerin sunayen masallatan da gwamnatin Kano ke biyan limaman su da ladanan su alawus-alawus duk wata.
Ya shaida wa wakilin mu cewa kuma hulɗar da ya ke yi da mutanen arziki ta da ko za a yi wata uku ba a biya albashi ba, to shi ko gezau ba zai yi ba.
Da yawan ma’aikatan da aka tattauna da su, sun bayyana cewa rashin biyan su albashi da Gwamnatin Kano ta yi daidai lokacin Sallah, duk kuwa da cewa watan Afrilu ya ma ƙare, hakan ya sa wasun su da dama sun riƙa maula ko neman bashin neman kuɗin abincin Sallah, domin su rufa wa iyalansu asiri, kada a ji kunyar maƙauta.
Wani mazaunin Fagge, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an bar ma’aikatan cikin yunwa da fatara a lokacin Sallah.
“Lamarin bai yi mana daɗi ba. Sallah ta zo mana a birkice.” Ya ce ko kayan Sallah ma kasa saye ko ɗunka wa ‘ya’yan sa ya yi.
Ya ce abin takaici ma shi ne da aka bar su kullum cikin zaman zullumi da tsammanin za a biya su. Aka ƙi sanar da su tun da wuri cewa ba za su samu albashi kafin Sallah ba.
PREMIUM TIMES ta kira Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba, amma bai ɗauki waya ya amsa kiran ba.
An kuma kasa samun Shugaban Kungiyar Kwadago (NLC) na Jihar Kano, Kabiru Minjibir, domin a ji ta bakin sa.