Rundunar ƴan sanda jihar ta kama wata mota kirar Maesandi cike makil da kayan haɗa nakiya da harsasai da bindigogi biyu.
Kakakin rundunar ƴan sanda jihar Kano Abdullahi Kiyawa ne ya sanar da haka a lokacin da yake bayyanaw wa manema labarai kamun da rundunar ta yi.
” Mun samu bayanan sirri game da wannan mota. Daganan muka fara bin motar. Jami’an mu sun kama motar a unguwar Bubbugaje dake ƙaramar hukumar Kumbutso dake jihar Kano.
Cikin abubuwan da aka samu a cikin motar akwai na’ura da sanadarn haɗa bom ɗin nukiliya, sinadaran haɗa bamabamai, harsasai madu dimbin yawa da bindigogi biyu.
Sai da kuma da direbar motar ya ga ba zai iya ba a lokacin da ƴan sanda ke bin sa. Sai ya ya ajiye motar ya arce.
Ƴan sanda na farautar a yanzu haka.