Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da ana bin ƙa’idojin yin gini a Nijeriya.
Ta faɗi haka ne a saƙon jaje da ta aika wa gwamnatin Jihar Legas da iyalan waɗanda su ka rasu a wani haɗarin rugujewar bene a Legas.
Rahotanni sun ce benen mai hawa 3, wanda ya ruguje a daren Lahadin makon jiya a unguwar Ebute-Metta, da ma can hukuma ta yi masa alamar za ta rushe shi saboda ta ga alamun ya susuce, to amma masu zama a cikin sa su ka ƙi tashi.
Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun garzaya wajen ginin bayan ya rushe don aikin ceton rai tare da haɗin gwiwar Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Jihar Legas da Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (SEMA) da kuma ‘yan sanda. Sun yi ƙoƙarin ceto mutum 23 yayin da mutum 8 su ka mutu a cikin ginin.
Ma’aikatan agajin sun ci gaba da aikin ceto da bincike don tserar da waɗanda su ka maƙale a cikin ginin.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai da ta fitar, mai taimaka wa ministar kan yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze, ta ce Hajiya Sadiya ba ta ji daɗin yawaitar bala’o’i da za a iya yi wa rigakafi irin wannan a ƙasar nan ba, kuma ta yi kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su yi aiki tuƙuru don rage aukuwar bala’o’in.
Ministar ta ce: “Wannan bikin Ƙaramar Sallah ne maras daɗi saboda rugujewar bene mai hawa uku a Legas. Ina jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Legas saboda wannan abin baƙin ciki.
“Ina yin addu’a ga iyalan waɗanda su ka rasa rayukan su a wannan gini da ya rushe da waɗanda aka ceto da ran su tare da jin raunuka a wannan lamari.
“Da jin labarin faruwar rugujewar ginin a Titin Ibadan a Ebute-Metta, Legas, mun umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su garzaya zuwa wajen tare da sauran hukumomin agaji da su ka dace. Abin baƙin ciki, mutane da dama sun maƙale a cikin ginin kuma an rasa rayuka da dama.
“Haka kuma ya na da muhimmanci cewa waɗanda haƙƙi ya rataya a wuyan su na tabbatar da ana gina ingantattun gine-gine a ƙasar nan su tabbatar da cewa an riƙa bin ƙa’idojin yin gini mai nagarta don kauce wa faruwar waɗannan abubuwan na baƙin ciki.”