Tsohon Gwamnan Jihar Legas, jigon APC kuma ɗan takarar shugaban ƙasa da ke son APC ta tsayar da shi a 2023, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya aikata ayyukan da su ka tabbatar da cancantar sa zama shugaban da Najeriya ke buƙata a 2023.
Tinubu ya bayyana haka a lokacin da ya gana da Gwamna Aminu Masari da kuma wakilan zaɓen ‘yan takarar APC a Katsina.
Tinubu wanda ya fito gadan-gadan neman APC tsayar da shi takarar gwabza karon zaɓen shugaban ƙasa, ya shaida wa Katsinawa cewa ya fito takara ne domin idan ya yi nasara, zai tabbatar da ya haɗa kan Najeriya.
Ya ce zai tsallakar da Najeriya daga siraɗin matsalar tsaro da ta tattalin arziki, ta yadda ‘yan Najeriya za su riƙa cin moriyar ɗimbin arzikin da ke shimfiɗe a cikin ƙasar.
Tinubu na takara ne tare da wasu makusantan siyasar sa na kusa, irin su Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Ahmad Lawan da Akinwumi Adesina da sauran su.
Rubdugun ‘Yan Takara: Kowa Ya Fito, Mulki Na Mai Rabo Ne -Tinubu:
Da ya ke magana kan yawan ‘yan takara, Tinubu ya ce kowa ma zai iya fitowa takara, amma fa a sani ba kowa zai zama shugaban ƙasa ba. Sai ka na da ƙwarewa, hangen nesa, horo da saitin iya samar da ci gaba. Ta yadda za ka fitar da ƙasa daga ƙangin faƙiranci zuwa tudun yalwa.
“An yi haka lokacin da Shugaba Buhari ke takara. Aka ce ba zai iya cin zaɓe ba. Amma da mu ka tashi haiƙan, sai ya yi nasara.
“A zaɓe na biyu kuma su ka juya masa baya. Mu kuma muka sake rufa masa baya ya yi nasara.” Inji Tinubu.
Tinubu ya yi alƙawarin idan ya zama shugaban ƙasa zai kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’i (ASUU).
“Ya zama dole a daina yajin aiki a jami’a. Kwas ɗin shekaru huɗu ya tsaya a shekaru huɗu kaɗai. Amma abin takaici yaran mu na shafe shekaru shida zuwa goma a jami’o’i. Ba zan yarda da wannan sagegeduwa ba.”
Gwamna Masari ya yabi Tinubu, ya ce jagoran su ne. Don haka ya cancanci kowa ya ba shi girman sa, ya girmama shi.
Masari ya yabi irin salon siyasar Tinubu ta rungumar jama’a, wanda ya ce ya zama inuwa, ba ka ƙyamar kowa.
Discussion about this post