Tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam’iyyar APC sannan ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa da a yi yarjejeniyar janye wa mutum ɗaya gara a fafata a fagen zaɓe mai rabo ka ɗauka.
Tinubu ya kara da yin kira ga wakilan APC da za su yi zaben fidda gwani su zaɓe shi saboda gogewarsa da kuma irin hidimar da yayi wa siyasa da kuma jam’iyyar APC.
Tinubu ya gana da wakilan jam’iyyar APC na jihar Taraba a garin Jalingo a cigaba da yake yi na ganawa da wakilan jam’iyyar da yake yi a faɗin kasar nan.
” Ina da yaƙini da tabbacin cewa zan lashe zaɓen fidda gwani, lallai ina da wannan yaƙini, ina tabbatar muku da haka.
Zuwa yanzu akwai ƴanntakara akalla 27 da suka sayi fom fin takarar shugaban kasa a APC, cikin su kuma harda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ministoci, gwamnoni da manyan ƴan siyasa.