Daga Fadar Shugaban Ƙasa har ofishin shugaban ƙaramar hukuma, kotu da sauran hukumomin gwamnati kowa ya san cewa ofishin Shugaban Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele bai amince wa duk mai riƙe da muƙamin ya tsoma hannu, ƙafa ko baki a sha’anin siyasa ba.
Amma kwatsam sai sunan Godwin Emefiele ya fara karaɗe soshiyal midiya, har ta kai ga wata ƙungiya ta manoma ta ce ta sai masa fam na takarar shugaban ƙasa na naira miliyan 100 cur.
Cikin watan Fabrairu PREMIUM TIMES ta bi sahun ‘ya Najeriya masu cewa ko dai Emefiele ya fito ya bayyana wa jama’a matsayin sa, ko kuma ya sauka daga shugabancin CBN.
Amma sai ya yi shiru, ya kauda kai daga kiraye-kirayen da ake yi masa. Hakan ya lokacin da labarin ƙungiyar Masu Noman Shinkafa ta ƙasa da abokan Emefiele aka ce sun haɗa kuɗi sun sai wa Emefiele fam na Naira miliyan 100.
Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Ƙasa Kan Rashawa (PACAC), Itse Sagay, ya bayyana cewa hankalin sa ya yi matuƙar tashi da ya ji cewa Emefiele na son fitowa takarar shugaban ƙasa.
Sagay ya ce idan ya yi haka ya karya dokar aiki.
Kiraye-kirayen Neman Emefiele Ya Yi Murabus:
Yayin da ake ci gaba da kiran Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sauka, shi ma Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya bi sahun masu kiran Emefiele ya ajiye aikin sa kawai. Ya ce lamarin zai gurgunta tattalin arzikin Najeriya. Kuma ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige shi.
Akeredolu ya buga hujja da Dokar Aikin CBN ta 1999 da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wadda ta haramta wa shugaban bankin tsoma baki cikin sha’anin siyasa.
Haka kuma jama’a da dama har da jam’iyyar PDP na ta kiraye-kirayen ko dai Emefiele ya sauka, ko kuma Buhari ya gaggauta tsige shi.
Wani mai rajin kare haƙƙin jama’a, Lauya Festus Ogun, shi kira ma ya yi bayan an tsige Emefiele, to EFCC ta fara gaggauta binciken irin gararumar da aka tafka a CBN a tsawon shekarun da Emefiele ya yi ya na mulki.
Ya nemi Buhari ya yi amfani da Sashe na 11(2) na Dokar CBN ya tsige Emefiele.
Ban Yanke Hukuncin Tsayawa Takara Ba Tukunna -Emefiele:
Daga ƙarshe dai ya yi magana cewa har yanzu bai yanke hukuncin tsayawa ba. Amma kuma ya gode wa masu neman ya tsaya ɗin.
Batun sayen fam kuma ya ce idan ya yi shawarar tsayawa, to shi da kan sa zai yi amfani da kuɗaɗen albashin sa da ya ke yin asusu ya na tarawa a tsawon shekaru 35 ya na aiki, ya sayi fam da su.
Zuwa yanzu dai sama da mutum 30 ke neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC. A cikin su kuma mutum 25 sun sayi fam na Naira miliyan 100 kowanen su.
Cikin watan Fabrairu PREMIUM TIMES ta buga ra’ayin ta cewa ko dai Gwamnan CBN Emefiele ya fito ya yi magana kan batun takarar sa ta shugaban ƙasa a 2023, ko kuma ya yi murabus.
Wannan ya nuna cewa an daɗe kenan ana ƙishin-ƙishin ɗin fitowar sa takarar.
A ra’ayin wa wannan jarida ta buga a lokacin, ta ce, a duk lokacin da batun zaɓen shugaban ƙasa ya kunno kai tun daga bayan samun ‘yanci har zuwa yau, har ɓarkewar Yaƙin Basasa, a kullum tashin hankalin da ke lulluɓe ruɗanin zaɓen sai ƙara muni ya ke yi.
Ta shiyyoyi da yankuna da dama tantagaryar ‘yan takifen maɓarnata da makasa ne sun tsare ƙofar shiga farfajiyar dimokraɗiyyar mu. A mafi yawan yankunan Arewa har zuwa Kudu, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ‘yan takife ne ke amfani da muggan makamai su na ƙoƙarin ganin sai sun kassara ƙasar nan. A lokaci ɗaya kuma su na ƙoƙarin sai sun durƙusar da tattalin arzikin ƙasar nan.
Ko ta ina a cikin ƙasar nan ana fama da rayuwar ƙunci da tsada. Ga matsalar rashin aikin yi sai ƙara ta’azzara ta ke yi. Fatara da talauci sai ƙara katutu su ke yi. Ƙarin abin takaici shi ne yadda farashin kusan komai ke ƙara hauhawa a ƙasar nan.
Romon-kunnen da aka yi kwanan nan aka ce malejin tattalin arziki ya cilla sama, ya ɗan bunƙasa, to cirawa saman da ya yi ba zai iya sa tatttalin arzikin ya yi tashi ba, kai ko gwauron numfashi ma ba zai iya yi ba.
Daɗin daɗawa kuma a daidai wannan lokaci da ake ta kiki-kaka da ƙadabolon yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa fitar da kitse daga wuta, balle a samu rangwamen da ta yi alƙawarin samarwa, an fara tunanin wanda zai gaji kujerar shugaban Najeriya a shekara mai zuwa. Daga cikin masu hanƙoron ganin sun hau kujerar, wani mutum ɗaya da ya ɗauki hankalin wannan jarida, shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Yayin da wasu ‘yan gararuma su ka fara ɓaɓatu da hayagagar cewa Emefiele ne ya cancanci zama shugaban ƙasa, saboda zai iya warware ƙabli da ba’adin da duk wata rabkanuwar da ta yi wa Najeriya da tattalin arzikin ta dabaibayi, PREMIUM TIMES na ganin cewa tatsuniya ce kawai ake yi, domin duk wata matsala da cukurkuɗewar da tattalin arzikin Najeriya ya yi, Godwin Emefiele ne ɗin nan ne dai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, tun daga 2014 har zuwa yau.
Mafarki ne kawai ake yi da soki-burutsu, a ce wai mutumin da ya kai darajar naira cikin kwazazabon ramin da ta kasa fita, kuma a ce shi ne zai gyara Najeriya.
Yayin da Emefiele ya karya Dokar Aikin CBN, ya bi ruɗin jagaliyar ‘yan siyasa a matsayin sa na Gwamnan CBN, lamarin kamar akwai lauje cikin naɗi. Bai kamata Emefiele ya ci gaba da zama gwamnan CBN ba. Kuma bai kamata a kare shi ba ya ci gaba da zama gwamna, kuma ya na siyasa.
Idan Emefiele na so ya fito takarar siyasa don neman kowane muƙami, hankali da tunani da ya kamata sun nuna bai kamata ya ci gaba da riƙe muƙamin sa na Gwamnan CBN ba. Sannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa har yau bai nesanta kan sa daga masu haƙilo da hanƙoron masu neman ya zama shugaban ƙasa ba.
A kan haka ne PREMIUM TIMES ke yin kira ga Emefiele ya girmama muƙami da kujerar Gwamnan CBN, ya sauka daga muƙamin, ya je ya yi siyasar sa. Idan kuma babu ruwan sa da batun takarar sa, to ya fito ya nesanta kan sa, su daina, a wuce wurin.
PREMIUM TIMES ta haƙƙaƙe cewa muddin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito ya fara neman kujerar shugaban ƙasa tun ya na kan aikin sa, to tabbas martaba da ƙimar wannan banki wanda shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya, ta zube ƙasa warwas.
Dama kuma tun za zaɓen 2015 aka fara nuna damuwar cewa CBN ya shiga hidimar zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen, da ma wasu zaɓukan baya.
Discussion about this post