Makonni biyu kafin a fitar da ‘yan takarar zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyu daban-daban, sama da mutum 40 ne gangariya masu neman maye gurbin da Shugaba Muhammadu Buhari zai bari bayan 2023. Waɗannan kuwa duk sun fito ne a cikin APC mai mulki da kuma PDP, babbar jam’iyyar Adawa.
Mutum 25 daga cikin 40 ɗin duk sun sayi tikitin takara na Naira miliyan 100 ne kowanen su, wato na jam’iyyar APC ya zuwa ranar Juma’a da dare, lokacin da aka rufe sayar da fam ɗin.
Sai dai kuma fam ɗin da aka ce an saya wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele su ka saya, ba a maida su ba. Hakan na nufin su biyu ɗin ba za su iya tsayawa takara a 2023 ba kenan.
Sannan kuma Ministan Ƙwadago Chris Ngige shi ma ya janye takarar shugaban ƙasa, sa’o’i kaɗan bayan Shugaba Buhari ya umarci ministocin sa 10 masu neman cewa su ajiye aiki kawai.
APC Za Ta Fara Tantance ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa:
Jam’iyyar APC ta aza ranar 23 Ga Mayu domin yi wa ‘yan takarar shugaban ƙasa zaman tantancewa a Abuja.
Akwai ‘yan takara da su ka kai har 25 masu neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC. Sun haɗa da irin su: Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Godswill Akpabio, Ogbonnaya Onu, Rochas Okorocha, Ibikunle Amosun
Sauran sun haɗa da Tunde Bakare, Ben Ayade, Dave Umahi, Kayode Fayemi, Emeka Nwajiuba, Ken Nnamani, Yahaya Bello, Mohammed Badaru da Ahmed Yerima.
Sai kuma irin su Timipre Sylva, Akinwumi Adesina da sauran su.
Mutum 17 Masu Neman Kujerar Shugaban Ƙasa Daga PDP:
Mutane 19 ne su ka sayi fam ɗin Naira miliyan 40 kowanen su a ƙarƙashin PDP. Amma Kwamitin Tantance ‘Yan Takara ya zubar da mutum biyu, saura 17 a yanzu.
Akwai Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed, Nyesom Wike da wasu da dama.
Babu Ruwan Mu Da Tsarin Karɓa-karɓa, Kowa Ya Fito Takara -PDP:
PDP ta rushe tsarin karɓa-karɓa, ta ce kowace shiyya na iya fitowa takarar shugaban ƙasa.
Yayin da zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa ke ƙara matsowa, jam’iyyar adawa PDP ta yanke shawarar yin watsi da tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya a 2023, inda ta ce ɗan kudu da ɗan Arewa, ɗan gabas ko ɗan yamma duk kowa zai iya fitowa takara.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka, jim kaɗan bayan da Kwamitin Ƙolin PDP ya tashi daga taron Majalisar Zartaswa da suka gudanar a ranar Laraba.
Ya ce an yanke wannan shawarar ce bisa tunanin bin umarni ko yin aiki da shawarar kwamitin tsarin karɓa-karɓa.
“Bayan an yi bayanai masu ƙarfi na tsawon lokaci, NEC na PDP sun amince da shawarar da Kwamitin Karɓa-karɓa na Ƙasa na PDP ya bayar, cewa a bar kowa ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023. Amma idan ta kama, jam’iyya za ta iya sa baki wajen ganin an cimma yarjejeniya tsakanin ‘yan takara, sun fitar da mutum ɗaya a cikin su, ba tare da sun kafsa a tsakanin su, a zaɓen fidda-gwani ba.”
Ya ce an cimma wannan matsaya ce domin shimfiɗa adalci, kuma don a samu isasshen lokacin da ya dace domin kafa tsarin yarjejeniyar karɓa-karɓa a lokaci mafi dacewa, ba tare da tunanin samun cikas ko wata farraƙa ba.”
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP ya ce za a yi gagarimin taron gangamin musamman na zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa a ranakun 28 da 29 Ga watan Mayu a Abuja.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata David Mark ne Shugaban Kwamitin Tsara Gangamin Zaɓen Ɗan Takarar PDP na 2023.
Yayin da Ifeanyi Ugwuanyi ke mataimakin Mark, tsohon Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema ne Sakatare.
Wannan sanarwar yin fatali da tsarin karɓa-karɓa ya zo ne makonni kaɗan Kwamitin Karɓa-karɓa ya miƙa rahoton da ya ƙunshi shawarwarin yin watsi da tsarin karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Kudu da Arewa.
Idan ba a manta ba, yankin Kudu maso Gabas ya daɗe ya na kartar ƙasa cewa su ya kamata a bai wa mulki a 2023.
Kwamitin karɓa-karɓar PDP dai na mutum 37, a ƙarƙashin shugabancin Gwamna Samuel Ortom ba Jihar Benuwai.
Tuni dai kwamitin tantance ‘yan takarar PDP a ƙarƙashin David Mark ya tantance ‘yan takarar PDP mutum 17, waɗanda su ka sayi fam na neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Yunƙurin Ƙaƙaba Jonathan Yin Takara A APC Bai Yi Nasara Ba:
Yayin da aka rufe sayar da fam ɗin takara a APC, ta tabbata dai Jonathan da Emefiele ba su maida ba su fam ɗin da aka sai masu ba.
An daɗe ana raɗe-raɗin cewa tsohon Shugaban Riƙon APC, Gwamna Mai Mala-Buni ya riƙa zawarcin Jonathan ya koma APC domin a ba shi takara, ya sake yin shekaru huɗu zango ɗaya kan mulki. Dabarar siyasa ce mai nuni da cewa idan Jonathan ya yi shekaru huɗu, to mulki zai sake komawa Arewa kenan.
Yayin da Jonathan bai ce ya koma APC ba, wata ƙungiya ta yi iƙirarin sai masa fam Naira miliyan 100, wadda daga baya ya nesanta kan sa daga ƙungiyar.
Makusanta na ganin Jonathan ya yi baya-baya daga tsayawa takara a APC, ganin yadda ya tsinci kan sa cikin ‘yan takara 25. Ya yi tsammanin shi kaɗai za a tsayar babu jayayya.
Yadda Za Ta Kaya A Zaɓen Fidda-gwani:
Yayin da ake ganin cewa bisa dukkan alamu APC za ta tsayar da ɗan Kudu ne takarar shugaban ƙasa, ita kuma PDP ta soke karɓa-karɓa, lamarin da ke nuni da cewa ɗan Arewa kan iya fito wa PDP takarar shugaban ƙasa kenan.
Wannan kuwa zai sauya hasashe da tunanin masu sharhi da nazarin siyasa da zaɓen ɗungurugum.
Yadda Buhari Ke Gwara Kawunan ‘Yan Shugaban Ƙasa Na APC:
Shugaba Buhari ya gama karantar masu neman takarar birjik a ƙarƙashin APC mai mulki.
Ya yi masu bazatar ba su umarnin duk wanda ke kan mulki ya gaggauta sauka, matsawar ya na da aniyar fitowa takara ko ma ta wane muƙami ne.
Ganin yadda aka umarce su sauka babu shiri, ana saura shekara ɗaya wa’adin mulkin su ya ƙare, ministoci da yawa sun janye takarar su.
Baya ga Chris Ngige, akwai Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda shi ma ya janye daga takarar gwamnan jihar Kebbi a 2023.
Dama kuma Buhari ya bai wa ‘yan APC mamaki, lokacin da ya naɗa Gwamna Buni shugabancin riƙon APC, bayan an tsige Adams Oshiomhole a gaban sa wurin taron shugabannin jam’iyyar a Abuja.
Sai kuma yadda ya sake yi masu bazatar naɗa Gwamna Sani Bello na Jihar Legas riƙon ragamar APC, daidai lokacin da ruwan rikici ya kusa nutsewa da Mala Buni.
Sai kuma yadda Buhari ya shammace su a baya-bayan nan. Ya bari sai da masu neman shugabancin jam’iyyar APC su ka sayi fam-fam ɗin shiga takara, amma daga ƙarshe ya tsaya kai-da-fata, ya ce Abdullahi Adamu za a naɗa shugaban APC na ƙasa. Kuma hakan aka yi.
Yunƙurowar Sanata Ahmed Lawan Takarar Shugaban Ƙasa:
Sanata Ahmad Lawan ya kutso kai a ranar Litinin, inda shigowar sa ta sa masu neman takarar shugaban ƙasa daga Arewa su ka cika huɗu: Akwai Yahaya Bello, Mohammed Badaru, Ahmed Sani Yarima da kuma shi Sanata Lawan, wanda shi kaɗai ne ɗan takara daga Arewa maso Gabas.
Tasirin NNPP Wajen Zaizayewar Fentin APC A Kano:
Yayin da zaɓen fidda-gwani ke ƙara gabatowa, manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP na fuskantar gagarimar matsala.
A gefe ɗaya PDP ta yi tsaye cak a cikin tasha babu fasinja, ita kuwa motar APC da rigaya ta cika maƙil da lodi, manyan fasinjojin cikin ta sai sauka su ke yi sanadiyyar rikicin da ya ɓarke tsakanin mai mota, direba, ‘yan kamasho da ‘yan ka-yi-na-yi, waɗanda su ka yi mata lodi.
Bisa dukkan alamu NNPP za ta kawo wa jam’iyyun biyu babbar matsala a zaɓen 2023, ganin yadda masu fita daga motar APC da ta PDP na sungumar kayan su su na shiga motar NNPP.
Babu ɗan takarar shugaban ƙasa da zai yi murna da rashin nasarar sa a Kano, jihar da ta fi kowace jiha samun yawan masu jefa ƙuri’a.