Daidai lokacin da saura shekara ɗaya mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙare, wanda a tsawon shekaru bakwai da ya shafe ya fi kowa ciwo wa ƙasar nan bashi, shugaban ya bayyana cewa tattaunawar yiwuwar yafe wa ƙasashen Afrika bashi na kan hanya.
Ya ce manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na duniya na duniya na tattauna yiwuwar yafe wa ƙasashen Afrika bashin dala biliyan 650.
Buhari wanda ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ya bayyana haka ne a wurin buɗe taron kwanaki uku na Taron Kakakin Majalisun Tarayyar Ƙasashen Afrika da aka buɗe ranar Litinin a Abuja.
Kusan tun bayan hawan Buhari mulki Najeriya ta bazama ta na ciwo bashi a ƙasashe daban-daban domin yin ayyukan raya ƙasa. Wannan lamari kuwa a kullum sai ƙara janyo wa mulkin sa baƙin jini ya ke yi.
Buhari ya ce ya zame wa ƙasashen Afrika tilas su ciwo bashin domin yin wasu manyan ayyuka.
Ya ce Najeriya ta ciwo biliyoyin daloli bashi, waɗanda su ka ƙara haifar wa ƙasar wawakeken giɓi.
Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya yi tsokaci kan yadda sojoji ke yi wa mulkin dimokraɗiyya karan-tsaye a Afrika.
Ya ce murƙushe shugabannin dimokraɗiyya a Sudan, Mali, Gini da Chadi ya ƙara jefa dimokraɗiyya cikin bala’i a Afrika.
Gbajabiamila ya ce haka kuma idan al’ummar ƙasa su ka gane mulkin dimokraɗiyya ya kasa tsinana masu komai, to fa dimokraɗiyya zubar da ƙimar ta kenan kuma al’umma ba za su goyi bayan ta ba.”
Shugaban Bankin Bunƙasa Afrika AfDB, Akinwumi Adesina, ya yi jawabi inda ya ce tattalin arzikin Afrika ya samu koma baya da kashi 1.5 sanadiyyar ɓarkewar korona a duniya.
Discussion about this post