Akalla mutum 360 ne ‘yan bindiga suka kashe daga watan Janairu zuwa Maris ɗin 2022 a jihar Kaduna.
Wannan bayani na kunshe ne a rahoton bayanai game da tsaron jihar wanda kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya gabatar a gidan gwanatin jihar a cikin makon jiya.
Rahoton ya nuna cewa a cikin mutum 360 din da aka kashe akwai mutanen da aka kashe a lokacin rikicin kabilanci.
A shekarar 2021 ‘yan bindiga sun kashe mutum 1,192 sannan sun yi garkuwa da mutum 3,348 a jihar.
Rahoton ya nuna cewa adadin yawan mutanen da aka kashe a shekarar 2020 ya fi yawan waɗanda aka kashe a jihohin dake Arewa maso Yammacin kasar nan.
Maharan sun kai wa jami’ar NDA da Kwatas din FAAN dake Kaduna.
Rahoton ya nuna cewa an yi garkuwa da mutum 1,389 daga watan Janairu zuwa Maris 2022 a jihar.
Birnin Gwari an yi garkuwa da mutum 169, Giwa -158, Igabi- 263, Chikun- 287 da Kajuru -203.
An yi garkuwa da mutum 249 a yankin Kudancin Kaduna.
An kuma yi wa mata 10 fyade inda a ciki shida ba su kai shekara 18 ba.
Mutum 258 sun ji rauni sannan an saci dabbobi 3,251 inda a ciki an sace 3,137 a yankin Kaduna ta Tsakiya.
Rundunar sojin ƙasa sun kashe ‘yan bindiga 41 ta kashe ‘yan bindiga 60 a jihar.
“Dakarun sun kama bindigogi 18 kirar AK-47, bindiga kirar sub-machine guda 7, bindiga kirar ‘pump action’ guda 5, harsashin bindiga kirar AK-47 guda 22, harsashin bindiga kirar ‘pump action’ guda 254, da harsasai 1,195.
Aruwan ya ce maharan sai sun yi mankasa da muggan kwayoyi kafin su kai farmaki.
Idan ba a manta ba a ranar 28 ga Maris ne ‘yan bindiga suka tare jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna inda suka kashe mutum 8 sannan suka yi garkuwa da mutum 168 daga cikin fashinjoji 970 dake cikin jirgin.