• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Abubuwan da ya kamata a sani game da tsarin amfani da dabaru biyu wajen yin rajistar masu zabe – Nazarin DUBAWA

    INEC ba za ta rufe rajistar zaɓen 2023 a ƙarshen Yuni ba – Farfesa Yakubu

    Buhari ya rantsar da sabon Cif Joji na riƙo

    Teacher

    Gwamnati ta umarci makarantu su fara amfani da Tsarin Ƙara wa Malamai Shekarun Ritaya

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    ‘Yan sanda sun damke dan shekara 30 din da ya nemi yi wa dattijiya mai shekaru 75 fyade

    Petrol Tankers

    ƊAN KUKA MAI JA WA UWAR SA JIFA: Ƙungiyar IPMAN ta ce ba za ta iya ci gaba da sayar da fetur a garuruwan yankin Igbo ba

    ZARGIN ƘARFA-ƘARFA A SIYASAR ENUGU: Sanata Ekweremadu ya saka takalmin ficewa daga PDP zuwa APC

    An kama Sanata Ekweremadu da matar sa a Landan, bisa zargin yunƙurin cire ƙodar wani ƙaramin yaro

    2023: APC ta ƙara wa’adin ranakun zaɓen fidda ‘yan takarar gwamna, sanata da na wakilan jihohi da tarayya

    KOWAR HAƊIYI TAƁARYA: Shugaban APC ya gana da Sanatocin APC domin magance fitar-farin-ɗango da ake yi daga jam’iyyar

    RAHOTO: Akalla ‘ƴan Najeriya miliyan 48 ne ke ƙantara kashi ‘bahaya’ a waje

    Woman Handcuff

    DUBU TA CIKA: An cafke Kabiru da ke yin lalata da ƴara ƙanana ta dubura a Abuja

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

RANAR IYALAI TA DUNIYA: Ma’aikatar Jinƙai za ta agaza wa iyalai mabuƙata 30

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 17, 2022
in Babban Labari
0
Ma’aikatar Jinƙai za ta shigar da ƙarin yara miliyan 5 a shirin ciyar da ƴan makaranta kafin 2023 -Minista Sadiya

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta kai wa aƙalla iyalai 30 da ke cikin ƙuncin rayuwa ɗauki.

Ta bayyana haka ne a ranar Litinin domin bikin Ranar Iyalai ta Duniya (International Day of Families) ta 2022, a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar ta bayar, wato Madam Rhoda Ishaku Iliya.

Ministar ta ce babban burin ma’aikatar shi ne ta inganta yanayin rayuwar iyalai, da masu fama da fatara da rashin galihu a cikin al’umma.

Hajiya Sadiya ta ce: “Inganta rayuwar iyalai talatin ɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da wannan ma’aikatar ke yi wajen kyautata rayuwar iyalai a ƙasar nan saboda Ranar Iyalai ta Duniya.

“Wasu daga cikin nasarorin da ma’aikatar ta samu ta fuskar kyautata rayuwar iyalai sun haɗa da bincikowa tare da sake haɗa fuskokin iyalan da su ka daɗe ba su ga juna ba, ƙarfafa rayuwar iyalai, sulhunta ma’auratan da su ka samu saɓani, saisaita iyalan da ke zuwa aiki, da samar da rancen kuɗi domin yin sana’a.”

Ministar ta yi nuni da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya, a cikin Ƙudirin ta mai lamba 47/237 wanda ya fara aiki daga shekarar 1993, ita ce ta ware ranar 15 ga Mayu na kowace shekara a faɗin duniya domin membobin majalisar su yi bikin Ranar Iyalai ta Duniya.

Ta yi bayanin cewa manufar Ranar Iyalai ta Duniya ita ce ta samar da wayar da kan jama’a da ƙara masaniya kan yadda tsarin zamantakewa da tattalin arziki ke shafar iyalai a ko’ina a duniya.

A cewar ta, kula da wannan ranar za ta ƙara wayar da kan jama’a dangane da al’amuran da su ka shafi iyali a matsayin su na cibiyar farko kuma ginshiƙin gina al’umma.

Ta ƙara da cewa ware ranar ya kuma nuna muhimmancin da ƙasashe su ka ɗora kan iyalai da halin da su ke ciki a duniya.

Yayin da ta ke nanata jigon Ranar Iyalai ta Duniya ta 2022, wato “Iyalai da Tsarin Zaman Birni” (“Families and Urbanisation”), ministar ta ce jigon zai ƙara wayar da kan al’umma kan muhimmancin inganta rayuwar iyali – wajen kyawawan tsare-tsaren zaman birni.

Ta ce: “Tsara zaman birni ya na daga cikin manyan ayyukan da su ka shafi duniyar mu da kyautatuwar rayuwar iyalai a faɗin duniya.

“Inganta zaman birni ya na da alaƙa da nasarorin da ake samu a ɗaya daga cikin Ƙudirorin Inganta Cigaban Rayuwa, wato ‘Sustainable Development Goals’ (SDG) da manufofi irin su SDG 1 (rage fatara), SDG 3 (kyakkyawan kiwon lafiya da jin daɗin rayuwa); SDG 11 (kyautata zaman mutane a birane ta fuskar zaman tare, zaman lafiya, juriya da ɗorewa), da SDG 10 (rage fifiko a zaman jama’a a tsakani da kuma cikin ƙasashe).

“Dukkan waɗannan manufofi da aka lissafa sun dogara ne kan irin yadda aka gudanar da tsare-tsaren zaman birni domin amfanar iyalai da inganta zamantakewar mutane masu bambancin shekaru da ke zaune a cikin birane.”

Hajiya Sadiya ta yi kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya sadaukar da bikin Ranar Iyalai ta Duniya ta bana ga neman maganin matsalolin da su ka shafi ɗorewar iyalan Nijeriya tare da cigaban su.

Ta ce: “Ina kira ga dukkan iyalan Nijeriya da su tashi tsaye wajen sa ido sosai tare da yin addu’o’i domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ƙasar mu ke fuskanta a yau da yadda su ka tarwatsa al’ummomi.”

Ministar ta yaba da irin damuwa da kuma goyon bayan da ƙungiyoyi masu zaman kan su da hukumomi na duniya da sauran masu ruwa da tsaki su ke bayarwa wajen kula da Ranar Iyalai ta Duniya.

Ta yi kira ga jihohi da ƙananan hukumomi da kuma ƙungiyoyi masu zaman kan su da su yi amfani da ƙarfin ikon su tare da fito da wasu shirye-shirye wajen yin bikin wannan ranar.

Haka kuma ta yi kira ga iyalai da su riƙa sa ido kan abubuwan da ‘ya’yan su ke aikatawa don tsare su daga faɗawa cikin tarkon masu amfani da yara da matasa wajen aikata laifuffuka a cikin al’umma.

Tags: AbujaFarouqHausaIyalaiNewsPREMIUM TIMESSadiya
Previous Post

Zan yi wa matsalar tsaro kifa ɗaya kwala ne idan aka zaɓe ni shugaban kasa – Amaechi

Next Post

TSADAR ABINCI A CIKIN ƘUNCIN RAYUWA: Farashin kayan abinci ya ƙaru da kashe 18.8%

Next Post
Gwamnatin Borno ta gargadi mutane kada su rika siyar da abincin tallafi da gwamnati ke raba musu

TSADAR ABINCI A CIKIN ƘUNCIN RAYUWA: Farashin kayan abinci ya ƙaru da kashe 18.8%

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHIRYE-SHIRYEN ZAƁEN 2023: INEC ta yi wa ƙarin mutum fiye da miliyan 10 rajista
  • SUN CI TALIYAR ƘARSHE: Sanatoci 58 da ba za su koma Majalisar Dattawa a zaɓen 2023 ba
  • INEC ba za ta rufe rajistar zaɓen 2023 a ƙarshen Yuni ba – Farfesa Yakubu
  • Buhari ya rantsar da sabon Cif Joji na riƙo
  • MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA: Har yanzu haƙa ta bata cimma ruwa ba, ina nan ina lalube – Tinubu

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.