Hukumar Daƙile Manyan Laifukan Zamba ta Birtaniya (NCA) ta bayyana ƙwato dala miliyan 23.5 waɗanda aka sata daga Najeriya lokacin mulkin sani Abacha.
An ƙwace kuɗaɗen daga hannun ɗan da Mohammed Abacha da kuma wani kamfanin gare mai suna Mecosta Securities Inc.
Haka dai Hukumar Daƙile Manyan Laifukan Zamba ta Birtaniya (NCA), ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Binciken ƙwaƙwaf ɗin da PREMIUM TIMES ta ƙara yi kan wasu kwafen takardun bayanai sun nuna asusun ajiyar kamfanin Mecosta na Landan, wanda aka bankaɗo kuɗaɗen satar a ciki, asusun na Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ne ke kula da shi.
A cikin shekarun 1990s Bagudu ya zama wani dillali, ɗan kamasho kuma mai lodi da jigilar maƙudan kuɗaɗen da Abacha ke karkatarwa ƙasashen waje. Bagudu ake bai wa kuɗaɗen ya na kimshewa a can.
A ranar 5 Ga Mayu, Hukumar NCA ta Birtaniya ta bayyana cewa Gwamnatin Birtaniya ta ƙara bankaɗo dala miliyan 23 da makusanta da iyalan Abacha su ka sata, su ka ɓoye a Ingila.
Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta bayyana bankaɗo waɗansu kuɗaɗe har dala miliyan 23.5, waɗanda aka tabbatar makusanta da iyalan tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Sani Abacha ne su ka saci kuɗin daga Najeriya su ka ɓoye a Ingila.
An gano kuɗaɗen waɗanda su na daga cikin maƙudan kuɗaɗen Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce an shafe shekaru a cikin 1990s ana jida daga Najeriya ana ɓoyewa ƙasashen waje.
Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta ce Abacha ne da makusantan sa da iyalan sa su ka riƙa kinshe kuɗaɗen a waje.
Haka dai hukumar ta bayyana a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis.
Har ila yau NCA ta ce an ƙwato kuɗaɗen ne bayan da Ma’aikatar Shari’ar Amurka wato USDOJ ta bada umarnin a tilasta ƙwace kuɗaɗen, bayan an shafe shekaru kusan bakwai ana karankatakaliyar shari’a.
NCA ta ce a yanzu dai an ƙwace kuɗaɗen kuma an maida su a hannun kulawar Hukumar Harkokin Cikin Gidan Birtaniya, wadda ita kuma tuni ta fara shirye-shiryen damƙa kuɗaɗen a hannun Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Amurka (USDOJ).
Babban Jami’in Kula da Ƙwato Kadarori Billy Beatie ya ce ƙwato dukiyar da manyan ‘yan siyasa da masu mulki ke sayewa babban aiki ne mai muhimmanci kuma babban makamin yaƙi da cin hanci da rashawa.
Yadda Aka Gano Kuɗaɗen A Asusun Kamfanin Bagudu Da Mohammed Abacha:
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Hukumar Daƙile Manyan Laifukan Zamba ta Birtaniya cikakken bayanin yadda su ka bankaɗo kuɗaɗen.
Ga Amsar NCA Zuwa Ga PREMIUM TIMES:
“An bankaɗo waɗannan kuɗaɗe daga Mohammed Sani Abacha da kamfanin Mecosta Securities Inc.” Inji Hukumar NCA, cikin wasiƙar da Jami’in Yaɗa Labaran NCA na Birtaniya ya aiko wa PREMIUM TIMES ta emel.
Daga nan ne kuma PREMIUM TIMES ta kakkaɓo harƙallar da Pandora Papers ta fallasa su Atiku Bagudu a baya, har ta kai ga an taɓa tsare Gwamnan na Kebbi a yanzu, kurkukun Amurka tsawon watanni shida.
Su Bagudu: Gungun’Yan-takifen Kifar Da Haƙƙin Talakawa:
Wannan gagarimin labari ne a kan yadda manyan ɓerayen Najeriya ke satar maƙudan kuɗaɗe, su na jibgewa ƙasashen waje, a lokacin da talakawan ƙasa ke sharar ɓarci bayan sun gama gaganiyar neman abincin magance yunwar rana ɗaya wadda su ka tsinci kan su bayan masu sace kuɗaɗen kuɗin ƙasa sun jefa su cikin kwazazzabon ƙuncin rayuwa.
Shekaru 11 da su ka gabata, a lokacin da Gwamnan Jihar Kebbi na yanzu, Abubakar Bagudu ke Sanata, ya tura wata tawagar ‘yan ƙaƙudubar sa zuwa ƙasar Singapore. Ya tura su ne domin su samo masa wurin da zai ɓoye wasu ƙazaman biliyoyin kuɗaɗe.
Waɗannan kuɗaɗe dai a yanzu haka su ne ake tafka kwatagwangwamar shari’a a Amurka, sakamakon bankaɗo kuɗaɗen da aka yi, kuma mahukuntan Amurka ke ƙoƙarin ƙwace su daga hannun Bagudu.
Masu bincike sun gano cewa kuɗaɗen da Bagudu ya ɓoye su na cikin biliyoyin dalolin da ya taimaki iyalan marigayi Shugaba Janar Sani Abacha su ka ɓoye bayan sace su daga Najeriya, a cikin shekarun 1990s.
Bagudu ya samu wani kamfani mai suna Asiaciti Trust, domin ya ɗauki gaban-gabarar aikin ɓoye masa ƙazaman kuɗaɗen a Singapore.
Shi dama Asiaciti Trust, wanda babban kamfanin lauyoyi ne, ya shahara wajen lauyar wa ɓarayin gwamnati ƙazaman kuɗaɗen da su ka sato daga ƙasar su zuwa wata ƙasa.
Domin ko a baya-bayan nan cikin Yuli 2020, sai da Hukumar Sa-ido Kan Hada-hadar Kuɗaɗe a Singapore ta ci Asiaciti Trust tarar dala miliyan 1.1 saboda wani laifin karya doka. Sun aikata laifin tun a cikin 2007 da 2008.
Asiaciti Trust sun taimaka wa Atiku Bagudu ya kafa kamfanonin ɓoye ƙazaman kuɗaɗen sata a ƙasashe uku da su ka haɗa da Singapore, Cook Islands da Birtaniya.
An rubuta sunayen Atiku Bagudu, matar sa, ‘ya’yan sa bakwai da ɗan’uwan sa Ibrahim a matsayin masu haƙƙi kan dukiyar.
A cikin 1988 Abacha ya mutu, kuma zuwa 2020 an dawo da dala biliyan 3.6 na ƙananan kuɗaɗen da su ka sata, su da babban gogarman ɗan-fiton su Atiku Bagudu, wanda a yanzu shi ne Gwamnan Jihar Kebbi.
Tsare Atiku Bagudu A Kurkukun Amurka:
Cikin 2003 an bankaɗo dala miliyan 163 a hannun Bagudu a Jersey, har aka tsare shi watanni shida. Ya cimma yarjejeniya da masu gabatar da ƙara aka maido kuɗaɗen Najeriya, shi kuma ya nemi kada a maida shi Najeriya, tunda ya biya kuɗaɗen.
PREMIUM TIMES HAUSA ta taɓa buga labarin ɗaure Bagudu a kurkukun Amurka, saboda mahukuntan ƙasar sun gano ƙasurgumin ɓarawon kuɗaɗen gwamnatin Najeriya ne.
Sannan kuma dala miliyan 308 da aka bankaɗo cikin 2020, su ma Atiku Bagudu ne ya karkatar da su.
Atiku ya yi tsamo-tsamo cikin harƙallar karkatar da ƙananan biliyoyin dalolin satar Abacha a bankunan ƙasashen Virgin Islands, Ingila, Guensey da Jersey.
Su Bagudu: Gungun ‘Yan-takifen Kifar Da Haƙƙin Talakawa:
Wannan kuma wani gagarimin labari ne a kan yadda manyan ɓerayen Najeriya ke satar maƙudan kuɗaɗe, su na jibgewa ƙasashen waje, a lokacin da talakawan ƙasa ke sharar ɓarci bayan sun gama gaganiyar neman abincin magance yunwar rana ɗaya wadda su ka tsinci kan su bayan masu sace kuɗaɗen kuɗin ƙasa sun jefa su cikin kwazazzabon ƙuncin rayuwa.
Shekaru 11 da su ka gabata, a lokacin da Gwamnan Jihar Kebbi na yanzu, Abubakar Bagudu ke Sanata, ya tura wata tawagar ‘yan ƙaƙudubar sa zuwa ƙasar Singapore. Ya tura su ne domin su samo masa wurin da zai ɓoye wasu ƙazaman biliyoyin kuɗaɗe.
Waɗannan kuɗaɗe dai a yanzu haka su ne ake tafka kwatagwangwamar shari’a a Amurka, sakamakon bankaɗo kuɗaɗen da aka yi, kuma mahukuntan Amurka ke ƙoƙarin ƙwace su daga hannun Bagudu.
Masu bincike sun gano cewa kuɗaɗen da Bagudu ya ɓoye su na cikin biliyoyin dalolin da ya taimaki iyalan marigayi Shugaba Janar Sani Abacha su ka ɓoye bayan sace su daga Najeriya, a cikin shekarun 1990s.
Bagudu ya samu wani kamfani mai suna Asiaciti Trust, domin ya ɗauki gaban-gabarar aikin ɓoye masa ƙazaman kuɗaɗen a Singapore.
Shi dama Asiaciti Trust, wanda babban kamfanin lauyoyi ne, ya shahara wajen lauyar wa ɓarayin gwamnati ƙazaman kuɗaɗen da su ka sato daga ƙasar su zuwa wata ƙasa.
Domin ko a baya-bayan nan cikin Yuli 2020, sai da Hukumar Sa-ido Kan Hada-hadar Kuɗaɗe a Singapore ta ci Asiaciti Trust tarar dala miliyan 1.1 saboda wani laifin karya doka. Sun aikata laifin tun a cikin 2007 da 2008.
Gungun ‘Yan Ta-kifen Kifar Da Talakawa:
A ranar 23 Ga Fabrairu, 2010, tawagar Bagudu wadda ta ƙunshi ƙanin sa Ibrahim Bagudu da wani tantirin lauya ɗan Landan, mai suna Ben Davies na Ofishin Lauyoyin Byrne & Partners sun haɗu da jami’an ƙaƙudubar Asiaciti Trust su ka yi wa dukiyar Atiku Bagudu rajistar sirrin yadda za a riƙa ɓoye ta asiri rufe.
An ɗora wa Asiaciti Trust aikin karkatar da ƙaramar dukiyar da Atiku Bagudu ya ɓoye a cikin 1997 a wani kamfanin sa mai suna Ridley Trust and Ridley zuwa cikin Asiaciti Trust daga Tsibirin Virgin Islands zuwa Singapore.
Bayan ‘yan watanni an gabji dala miliyan 99 daga Ridley an gabza a Asiaciti Trust.
An dai san Atiku Bagudu a matsayin yaron iyalan da ke masu harƙallar ɓoye kuɗaɗen sata a ƙasashen waje. Ba a san yadda aka yi shi ma ya narke ya zama gogaggen jan-wuyan da ya riƙa ɓoye na sa kuɗaɗen da ya riƙa gabza a harƙallar sata-ta-saci sata ba.
Pandora Papers gamayyar ƙungiyar wasu mashahuran ‘yan jarida ne na duniya da kungiyoyin fafutikar yaƙi da rashawa sama da 150. Akwai wasu ‘yan PREMIUM TIMES a cikin kungiyar.
Su ne ke aikin bankaɗo harƙallar da manyan ‘yan siyasa masu ci da na baya da sauran shugabanni su ka danne.