Yayin da kusan mutum 6,000 ke jiran a zartas masu da hukuncin kisa a wasu ƙasashen Sahara na Afrika, rahoton ya nuna cewa fiye da rabin masu wannan jiran zartas da hukuncin kisa duk a Najeriya su ke.
Aƙalla a wasu ƙasashen Afrika, ciki har da Najeriya akwai mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa har 5841, kamar yadda Ƙungiyar Amnesty International ta buga rahoto.
AI ta ce ya zuwa watan Disamba 2021, a Najeriya kaɗai akwai mutum 3036 waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa.
Adadin ya nuna kashi 52 bisa 100 na masu wannan jiran a zartas da kisa a kan su, duk a Najeriya su ke.
Kasar Kenya ce ta biyu mai adadin mutum 601, masu jiran kisa. Sai kuma Tanzaniya mutum 480. Sudan ta Kudu kuma akwai mutum 334.
Yayin da a Zambiya akwai mutum 257, Kamaru 250, Mauritaniya mutum 183, Ghana mutum 165 sai Uganda 135.
A Saliyo mutum 117 ke jiran a zartas masu da hukuncin kisa. A Sudan mutum 95, Zimbabwe 66, Mali 48, Malawi 37, sai Laberiya mutum 16 kacal.
Sai dai kuma duk da cewa doka ta amince a riƙa kashe wanda aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya da sauran ƙasashen, zartas da hukuncin ya na da wahala matuƙa.
A Najeriya an yanke wa mutum 56 hukuncin kisa cikin 2021, amma Amnesty International ta ce ba a kashe kowa a cikin shekarar ba.
“Tsakanin 2007 har zuwa 2017 mutum bakwai kaɗai aka zartas wa hukuncin kisa a kan su a Najeriya. Su ɗin ma, rabon da zartas da hukuncin a kan wani tun cikin 2016.” Inji AI.
Zartas Da Hukuncin Kisa A Duniya:
A cikin 2021 an zartas da hukuncin kisa kan mutum 579 a duniya. A cikin 2020 kuwa mutum 483 aka kashe.
Sai dai kuma duk da yawan adadin waɗanda aka zartas da hukuncin a kan su, Amnesty International ta ce ba a kashe da yawa ba idan aka kwatanta da adadin da aka sha zartas masu da hukuncin kisa a shekarun baya, kafin 2010.
Hukuncin Kisa A Duniya:
An yanke hukuncin kisa kan mutum 1,477 a duniya cikin 2020. A cikin 2021 kuwa kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutum 2,052 a duniya.
Sai dai kuma waɗannan adadi duk babu lissafin yawan waɗanda ake yanke wa hukuncin kisa a Chana, da kuma waɗanda Chana ɗin ke zartas masu da hukuncin kisan.
An haƙƙaƙe dai an fi zartas da hukuncin kisa bakatatan a duniya, fiye da sauran ƙasashe.
Koriya ta Arewa da Vietnam ma duk a asirce su ke zartas da hukuncin kisa, ba a sanin adadi.
Yayin da a cikin 2021 aka kashe mutum 314 a Iran, cikin watan Maris na 2022 a Saudiya an fille kawunan mutum 81 a rana ɗaya.
Discussion about this post