A cigaba da tsiyayewar da APC da PDP ke cigaba da yi a jihar Kano, NNPP ta yi babbar kamo a yau Laraba.
Sanara Ibrahim Shekarau ya canja sheka daga jam’iyyar ANPP ya koma jam’iyyar NNPP, jam’iyya mai alamar kayan marmari a Kano.
Wannan sauyi da aka samu ya girgiza jam’iyyar APC a jihar Kano ganin yadda jigajigan ta ke waskewa suna mannewa da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya ne fitaccen tsohon ɗan majalisa Jibrin Abdulmumini ya sauya sheka daga APC zuwa NNPP.
Rikici tsakanin bangaren sanata Shekarau da gwamnan jihar Kano taki ci ta ki cinyewa. Hakan yasa a karshe dai yanzu Shekarau dole ya canja Sheka daga APC zuwa NNPP.
Jim kadan bayan wannan sauyi da aka samu sai kuma jam’y ta mika wa Shekarau fom ɗin takarar Sanatan Kano.
Wani mai yin sharhi a harkar siyasar Kano, Murnai Ashafa ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa wannan gagarimar asara ce ga APC a jihar Kano.
” Ina so in tabbatar muku cewa da APC da PDP a Kano sun shiga ruɗu. Goguwar Kwankwaso sai ɗibar ƴan siyasa ta ke yi a runduna-runduna. Yanzu fa Kanawa NNPP suke yi. Goguwa ce ta dirkako Kano sai dai fa ayi hakuri kuma.
Discussion about this post