‘Yan bindigar da su ka yi garkuwa da ɗimbin fasinjojin da suka yi fashin jirgin ƙasa a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sun sake sakin wani bidiyo, mai ɗauke da wasu da ke hannun su, su na bayanin Gwamnatin Tarayya ta kai masu agaji, ta cece su daga hannun ‘yan Boko Haram ɗin.
Bidiyon wanda su ka saki a ranar Litinin, shi ne na biyar a jerin bidiyon da su ka saki, tun bayan kama matafiyan a ranar Litinin, 28 Ga Maris.
Yau Litinin ce waɗanda ake tsare da su ɗin su ka cika kwanaki 62 a hannun maharan.
Duk da Gwamantin Najeriya ta ce ta na bakin ƙoƙarin ta, har yau babu wata hoɓɓasa da za a iya tabbatar da cewa ta yi, domin ceto mutanen da ke tsare.
Cikin makon jiya ne su ka saki wata mata mai ciki, bayan ta tabbatar masu da cewa ta kusa haihuwa, kuma ritaya ake yi mata a lokacin haihuwa, ba da kan ta ta ke haihuwa ba.
A bidiyon da su ka saki yau Litinin, an nuno maza biyar durƙushe a bayan mata uku waɗanda ke zaune a kan tanfol.
Dan bindiga ɗaya ɗauke da bindiga ya gabatar da su, tare da ba su umarnin su yi magana ga Gwamnatin Tarayya.
Abin mamaki kuma shi ne yadda ɗan bindigar ke magana da Turanci. Amma sauran bidiyon huɗu da su ka yi magaba, duk da Hausa su ka yi.
Maryam Abubakar ta ce an kama ta tare da ‘ya’yan ta huɗu. Ta ce ‘ya’yan ta biyu a cikin huɗun ba su da lafiya.
Jawabin Ɗan Ango Abdullahi:
“Suna na Sadiq Ango Abdullahi. Mu na roƙon Gwamnatin Tarayya ta kawo mana ɗauki, ta cece mu. Yau kwanan mu 62 a hannun su, a cikin daji. Yawancin mu ba mu da lafiya, lamarin na ƙara taɓarɓarewa. A kawo mana ɗauki kafin mu kai ga rasa rayukan mu.”
Jawabin ‘Yar Ajin Su Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Ƙasa:
“Suna na Gladys, ina kira musamman ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo. Ni ajin mu ɗaya da shi a Makarantar Lauyoyi. Mu ne ‘yan ajin 1978/79.
“Ka tuna kai kaka ne, kuma uba ne. Ka kawo mana ɗauki, yau kwanan mu 62 kuma ina da ɗa na da ke kwance ya na jiyya. Yanzu haka ban san halin da ya ke ciki ba.” Inji ta.
Haka sauran duk su ka yi roƙo ga Gwamnatin Tarayya ta kai masu ɗauki.