‘Yan siyasar PDP da dama sun nuna kwaɗayin so zama gwamna a Jihar Sokoto, bayan cikar wa’adin Gwamna Aminu Tambuwal a Mayu, 2023.
Sai dai kuma har yau hankulan su bai natsu sun fahimci alƙiblar da za su dosa ba, saboda har yanzu ɗin nan Tambuwal bai nuna ɗan takarar da ya fi kwanta masa a rai ba.
Akwai ‘yan takara shida daga PDP, ciki akwai makusancin Gwamna na ƙut da ƙut, akwai kuma waɗanda su ka dogara kan wasu iyayen gidan su a jihar da cikin jam’iyya.
Ba kamar jihohin Kano da Katsina inda Abdullahi Ganduje da Nasir El-Rufai su ka bayyana khalifofin su, kuma su ka ce wa sauran ‘yan takarar su nemi wasu muƙaman, shi kuwa Tambuwal har yau bai nuna wanda ya fi kwanta masa a rai ba.
Yayin da wasu masu goyon bayan Tambuwal irin su Sani Ɗahiru na cewa ya nuna shi “cikakken majiɓincin dimokraɗiyya ne”, wanda ke son dimokraɗiyya ta yi aikin ta wajen fitar da ‘yan takara. Amma wasu kuma na ganin cewa Tambuwal kar ya ke kallon su, ya na da wanda ya fi kwanta masa a rai, sai lokaci ya ƙure sannan zai bayyana shi.
Su Wane Ne ‘Yan Takarar Gwamnan Sokoto A PDP?:
Na farko dai akwai Mataimakin Gwamna Mannir Ɗan Iya, wanda ɗan Hakimin Ƙware ne. Ya na da biyayya ga Gwamna, duk kuwa da cewa ba shi ne ubangidan sa a siyasa ba.
Mannir ne Mataimakin Gwamna, kuma Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu tun daga 2015 har zuwa 2022.
Akwai kuma Sagir Bagaraswa, tsohon Kwamishinan Muhalli, kuma ɗa ga Attahiru Bagarawa, tsohon Gwamnan Sokoto.
Sagir yaro ne, amma fa ya na da ɗimbin magoya baya a cikin matasa. Sannan kuma ya na tinƙaho ganin cewa mahaifin sa ubangidan Gwamna Tambuwal ne.
Akwai kuma Bello Goronyo, Shugaban PDP na Jihar Sokoto a yanzu. Tsohon kwamishina ne, kafin Tambuwal ya nemi ya je ya riƙe jam’iyya. Ya na da biyayya ga Tambuwal, kuma ya na da ɗimbin magoya baya.
Akwai kuma Muktar Shagari, ɗan uwan tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Shehu Shagari. Shagari shi kaɗai ya ke yaƙin sa, babu dakaru, babu ubangida. Tun cikin 1999 ya ke PDP, har yau kuma bai ji haushi ya taɓa canja sheƙa ba. Ya yi wa tsohon Gwamna Aliyu Wamakko Mataimakin Gwamna har tsawon shekaru takwas.
Shagari ya fi sauran cancanta idan ana maganar ilmi. Ya taɓa yin Minista a zamanin mulkin Obasanjo. Ana tsoron idan ya zama gwamna ba zai yi wa Tambuwal biyayya ba.
Na shida shi ne Sa’idu Umar, Ubandoman Sokoto. Ya yi Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto, ya yi Kwamishina, kuma tun daga 1999 zuwa yau, dukkan gwamnoni uku da aka yi a Sokoto, haihuwar ƙauye ne. Amma shi Sa’idu a cikin Sokoto aka haife shi.
Ya na da kusanci da masarauta, ‘yan siyasa da ‘yan boko.
Discussion about this post