Tsohon gwamnan jihar Abia, Atiku Abubakar ya gargaɗi jam’iyyar APC ta yi karatun ta natsu wajen zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Da yake mika sakon taya Atiku murnar nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP Kalu ya ce kada APC ta kuskura ta tsaida wani ɗan kudu ɗan takaran ta.
” Idan har ba ritayar dole APC take so ta tafi ba a siyasa, toh ta zaɓi ɗan Arewa ne yayi mata takarar shugaban kasa tunda wuri. Kuma Ahmed Lawan ne ya fi dacewa.
” Dalili kuwa shine, Ahmed Lawan ɗan yankin Arewa maso Gavas ne, tankin da Atiku ya fito. Hakan zai sa APC ta yi tasiri a zaɓen da za a yi a 2023.
Kalu ya ce a halin da ake ciki yanzu sai an sake yin nazari mai zurfi a lissafin da ake yi a jam’iyyar.
Idan ba a manta ba tsohon mataimakin shugban kasa Atiku Abubakar ne yayi nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi ranar Asabar a Abuja.
Ariku ya samu kuri’u 371, inda ya doke abokanan takarar sa, Nysom Wike, Bukola Saraki, Bala Mohammed, Emmanuel Udom na jihar Akwa-Ibom sai kuma Aminu Tambuwal da ya janye wa Atiku dab da za a fara kaɗa kuri’a.